Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa gwamnatin Jihar Neja da al’ummar ta kan mutuwar mutane a wani samame na daƙile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Wushishi/Lukoto.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce yanayin da ya jawo mutuwar mutanen yana buƙatar a gudanar da cikakken bincike cikin gaskiya da adalci.
Idris ya ce Gwamnatin Tarayya ta riga ta ɗauki matakan gano abin da ya faru, bayan da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya dakatar da Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Idris ya ce: “Matakin gaggawar da Mai Girma Ministan Harkokin Cikin Gida ya ɗauka yana nuna irin muhimmancin da Gwamnatin Tarayya ta bai wa wannan lamari. Za a bar binciken ya gano ainihin abin da ya faru, kuma gwamnati na tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa za ta ɗauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.”
Ya jaddada cewa duk da ci gaba da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da sauran ayyukan da suka saɓa doka, waɗanda ke barazana ga tsaron ƙasa, albarkatun tattalin arziki da muhalli, dole ne a gudanar da ayyukan tabbatar da bin doka bisa ƙa’ida tare da mutunta rayuwar ɗan’adam da mutuncin sa.
Ya ce: “Ba za a yi ƙoƙarin kare duk wanda aka samu da laifi ba. A lokaci guda kuma, bai kamata mu riga mu yanke hukunci kan sakamakon binciken ba. Nauyin gwamnati shi ne tabbatar da cewa an gano gaskiyar abin da ya faru kuma an yi adalci.”
Idris ya yi kira ga al’ummar Wushishi da sauran al’ummar Jihar Neja da su kwantar da hankalin su, tare da ba da damar gudanar da binciken ba tare da katsalandan ba.
Ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu, al’ummar Wushishi da kuma al’ummar Jihar Neja baki ɗaya, yana mai tabbatar musu da cewa za a gano cikakken abin da ya jawo wannan mummunan lamari.
Ya roƙi Allah Ya jiƙan waɗanda suka mutu, Ya bai wa iyalan su da al’ummar Jihar Neja ƙarfin jure wannan rashi.






