Babban Bankin Nijeriya (CBN), reshen Jihar Gombe, ya gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata domin bunƙasa shigar al’umma cikin harkokin kuɗi, ƙara wayar da kan jama’a game da ayyukan bankin, tare da karɓar ra’ayoyi kan manufofi da ayyukan sa.
An gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa da ke Gombe, inda ya haɗa jami’an gwamnati, masu ruwa da tsaki a fannin kuɗi, ‘yan kasuwa, ɗalibai da sauran jama’a.
Da yake jawabi wajen buɗe taron, Mai Kula da Reshen CBN na Gombe, Alhaji Yunusa Buba Mubi, ya ce an shirya bajekolin ne domin ƙarfafa hulɗa tsakanin CBN da jama’a ta hanyar wayar da kai, ilimantarwa da kuma karɓar ra’ayoyi kai-tsaye.
Mubi ya bayyana cewa wata tawaga daga hedikwatar CBN, ƙarƙashin jagorancin Mukaddashin Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a da Huldar Masu Zuba Jari, ta isa Gombe domin gudanar da shirin wayar da kan jama’a.
Ya buƙaci mahalarta taron su mai da hankali kan gabatarwar da za a yi, su yi tambayoyi masu amfani tare da bayar da shawarwari masu ma’ana domin taimaka wa bankin wajen inganta ayyukan sa da hidimomin sa.
A cewar sa, wannan shiri na daga cikin dabarun CBN na bunƙasa shigar al’umma cikin harkokin kuɗi, haɓaka ci gaban tattalin arziki da tabbatar da cewa manufofi da ayyukan bankin sun isa ga al’ummomin karkara a faɗin ƙasar nan.
Da take wakiltar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Hajiya Hakama Sidi Ali ta ce wannan baje-koli na daga cikin muhimman tsare-tsaren bankin na inganta rayuwa da hanyoyin samun abin yi na ‘yan Nijeriya ta hanyar ƙara ilimin harkokin kuɗi da faɗaɗa damar amfani da hanyoyin biyan kuɗi na zamani.
Ta ce CBN na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da daidaiton manufofin kuɗi da tsarin kuɗi, rage hauhawar farashin kayayyaki da tabbatar da daidaiton farashi bisa ga nauyin da doka ta ɗora masa, tana mai cewa waɗannan manufofi suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ɗorewar ci gaban tattalin arziki.
Shi ma da yake jawabi, Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, wanda Babban Sakatare a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Alhaji Salihu Adamu Sambo, ya wakilta, ya yaba wa CBN kan faɗaɗa ayyukan kuɗi na dijital, yana mai cewa hakan ya sa gudanar da harkokin kasuwanci ya zama mafi sauƙi, sauri da kuma dacewa ga ɗaiɗaikun mutane da ‘yan kasuwa.
Sai dai ya gargaɗi ‘yan Nijeriya da su guji aikata laifukan yanar gizo da sauran nau’o’in damfara waɗanda za su iya raunana amincewar jama’a da tsarin kuɗin ƙasar tare da kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki.
Tuni dai wannan tawaga da ta dira Bauchi, domin ci gaba da wannan gagarumin shirin wayar da kai da kuma jin ra’ayoyin jama’a.






