• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun kuɓutar da mutum 14, sun ƙwato dabbobi 281 daga hannun ’yan ta’adda

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 5, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun kuɓutar da mutum 14, sun ƙwato dabbobi 281 daga hannun ’yan ta’adda
Wasu daga cikin dabbobi 281 da sojoji suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Jihar Sakkwato

Wasu daga cikin dabbobi 281 da sojoji suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Jihar Sakkwato

Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya ta 8 sun samu gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga bayan sun kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato dabbobi 281 da aka sace a wani hari da aka kai ƙauyen Horo Birni da ke Ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.

Majiyar soji ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar jiya Talata, inda mazauna ƙauyen suka aika da kiran gaggawa bayan ’yan bindiga sun afka masu, suka yi awon gaba da mutane da kuma dabbobi.

Bayan samun rahoton, dakarun sojin suka nufi yankin ba tare da ɓata lokaci ba. Da suka cim ma maharan, sai aka gwabza musayar wuta mai zafi, lamarin da ya sanya ’yan bindigar suka watse domin tsira da rayukan su.

Majiyar ta ce sakamakon matsin lambar da sojojin suka yi musu, maharan sun gudu cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga, inda suka bar duk mutanen da suka yi garkuwa da su da kuma yawancin dabbobin da suka sace.

Wani dattijo tare da sojoji bayan an kuɓutar da shi daga hannun ‘yan bindiga a Jihar Sakkwato

Wani dattijo tare da sojoji bayan an kuɓutar da shi daga hannun ‘yan bindiga a Jihar Sakkwato

A cewar majiyar, dakarun sun yi nasarar ceto mutum 14 tare da ƙwato shanu 195, tumaki 84, raƙuma biyu da babura biyu, waɗanda ake kyautata zaton mallakin mazauna ƙauyen ne.

Ta ce gaggawar da jami’an sojin suka yi wajen amsa kiran neman agaji ce ta hana maharan cimma manufar su, tare da ba da damar ceto rayuka da kuma dawo da dukiyoyin al’umma.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa Rundunar Sojin Nijeriya za ta ci gaba da gudanar da samame da sintiri a sassan da ke fama da matsalar tsaro domin hana ayyukan ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuffuka.

Ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri da kuma kai rahoton duk wani abin da ke haifar da zargi, domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro.

Tags: 'yan bindigaHoro BirniJihar SakkwatoShagarisojojita'addanci
Previous Post

Manufofin Tinubu na bunƙasa masana’antu suna samar da ayyuka, ayyukan yi da ƙirƙire-ƙirƙire – Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Yadda tawagar wayar da kai daga CBN ta baje koli a Gombe, ta dira Bauchi domin ƙara shigar da jama’a cikin harkokin kuɗi da inganta cigaban tattalin arziki

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Yadda tawagar wayar da kai daga CBN ta baje koli a Gombe, ta dira Bauchi domin ƙara shigar da jama’a cikin harkokin kuɗi da inganta cigaban tattalin arziki

Yadda tawagar wayar da kai daga CBN ta baje koli a Gombe, ta dira Bauchi domin ƙara shigar da jama'a cikin harkokin kuɗi da inganta cigaban tattalin arziki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!