Yunƙurin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a faɗin Nijeriya ya sake samun ƙwarin gwiwa a yau, bayan da Majalisar Wakilai ta karɓi rahoton Kwamitin ta na Musamman kan Bita da Gyaran Kundin Tsarin Mulki game da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa rundunonin ‘yan sanda na jihohi.
Mataimakin Kakakin Majalisar kuma Shugaban Kwamitin Bita da Gyaran Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, shi ne ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisa, lamarin da ya share fagen muhawara da kuma yin nazari kan ƙudirin sashe bayan sashe daga hannun ‘yan majalisar.
Gabatar da rahoton ya biyo bayan zaman sirri da Kwamitin Bita da Gyaran Kundin Tsarin Mulki ya gudanar a ranar Litinin, inda membobin sa suka daidaita matsayin Majalisar Wakilai da na Majalisar Dattawa kan sigar ƙudirin dokar a matsayin wani ɓangare na ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulki.
Ƙudirin gyaran na neman yin kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi masa gyara), domin samar da “tsarin doka na kafa, tsarawa da gudanar da ayyukan rundunonin ‘yan sandan jihohi da sauran batutuwa masu alaƙa.”
Bisa tsarin majalisa, za a tsara ranar da za a yi nazari kan rahoton a wata ranar zaman majalisa mai zuwa, inda ake sa ran Kwamitin Dokoki da Harkokin Majalisa zai ƙayyade ranar muhawara da kuma yin nazari kan ƙudirin sashe bayan sashe.
Ƙudirin yana daga cikin muhimman ƙudirorin gyaran kundin tsarin mulki da ke gaban Majalisar Tarayya, yayin da gwamnatocin jihohi, masana harkokin tsaro da ƙungiyoyin fararen hula suke ci gaba da kira da a karkasa tsarin aikin ‘yan sanda domin magance matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a Nijeriya.
Masu goyon bayan ƙudirin na cewa kafa ‘yan sandan jihohi zai inganta tattara bayanan sirri, ya ƙarfafa tsarin tsaron al’umma, tare da ba da damar gaggauta mayar da martani ga barazanar tsaro a matakin ƙananan hukumomi da jihohi.
Sai dai masu adawa da shi sun nuna damuwa kan yiwuwar gwamnatocin jihohi su yi amfani da rundunar ta hanyar da ba ta dace ba, tare da jaddada buƙatar samar da ingantattun tanade-tanaden kundin tsarin mulki domin hana tsoma bakin siyasa.
A wani cigaba kuma, Majalisar Wakilai ta amince da rahoton Kwamitin ta kan Harkokin ‘Yan Sanda wanda ya amince da kasafin kuɗin Asusun Tallafa wa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya na shekarun 2025 da 2026.
Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin ‘Yan Sanda, Abubakar Yelleman, shi ne ya gabatar da rahoton, wanda aka yi nazari a kan sa kuma aka amince da shi yayin zaman Kwamitin Kasafi ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu.
Domin shekarar kasafin kuɗi ta 2025, ‘yan majalisar sun amince da kasafin kuɗi na naira biliyan 170.11 ga Asusun Tallafa wa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.
Rabe-raben kasafin ya nuna cewa an ware naira biliyan 27.29 domin ayyukan babban birnin Asusun Tallafa wa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, yayin da aka ware naira biliyan 132.45 domin manyan ayyukan cigaba na Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.
Haka kuma, kasafin ya tanadi naira biliyan 1.82 domin albashin ma’aikata da kuma naira biliyan 8.54 domin kuɗaɗen gudanar da ayyuka.
Haka zalika, Majalisar ta amince da naira biliyan 233.96 a matsayin kasafin kuɗin da aka gabatar ga Asusun Tallafa wa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya na shekarar kasafin kuɗi ta 2026.
Kasafin da aka amince da shi ya ƙunshi naira biliyan 43.78 domin ayyukan babban birnin Asusun Tallafa wa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, naira biliyan 179.11 domin manyan ayyukan cigaba na Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, naira biliyan 1.86 domin albashin ma’aikata da kuma naira biliyan 9.21 domin kuɗaɗen gudanar da ayyuka.
Ana sa ran ƙudirorin kasafin za su wuce karatu na uku a ranar Laraba kafin Majalisar Wakilai ta amince da su a hukumance.
An kafa Asusun Tallafa wa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ne ƙarƙashin Dokar Asusun Tallafa wa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, domin samar da ƙarin kuɗaɗe na horaswa, kayan aiki, dabarun sufuri da walwalar jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.
Asusun yana ƙara wa kuɗaɗen da ake ware wa rundunar a kasafin kuɗin shekara, kuma ana samun kuɗin sa ne daga rabon Asusun Tarayya, tallafi, gudunmawa da sauran hanyoyin da doka ta tanada.
Ƙarin kuɗaɗen da aka ware a kasafin shekarun 2025 da 2026 na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tarayya ke sabunta ƙoƙarin ta na ƙarfafa tsaron cikin gida, zamanantar da kayayyakin aikin ‘yan sanda da kuma inganta ƙwarewa da ƙarfin gudanar da ayyukan Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.






