• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Ebonyi za ta ƙayyade kuɗin haya, kuɗin dillalai da kasuwancin tarkacen ƙarafa

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
July 21, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Ebonyi za ta ƙayyade kuɗin haya, kuɗin dillalai da kasuwancin tarkacen ƙarafa
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Ogbonna Erishi Nwifuru

Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Ogbonna Erishi Nwifuru

Majalisar Zartarwa ta Jihar Ebonyi ta amince da miƙa wasu ƙudirin dokoki ga Majalisar Dokokin jihar domin tsara yadda ake karɓar kuɗin hayar gidaje, kuɗin dillalan gidaje, da kuma saye da sayarwar tarkacen ƙarafa da na’urorin lantarki a faɗin jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na jihar, Cif Ikeuwah Omebeh, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Centenary City, Abakaliki.

Omebeh ya ce ƙudirin dokar da ta shafi alaƙar mai gida da ɗan haya zai daƙile yadda dillalan gidaje suke karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, ta hanyar ƙayyade kuɗin dillanci zuwa kaso biyu cikin ɗari (2%) kacal na jimillar kuɗin hayar da ɗan haya ya biya.

Ya bayyana cewa an tsara matakin ne domin kare mazauna jihar daga tsadar kuɗaɗen da ake cazar su, tare da tabbatar da cewa ƙwararru kuma masu rijista ne kaɗai za su gudanar da harkar dillancin gidaje a jihar.

Kwamishinan ya ce ƙudirin doka na biyu zai tsara yadda ake saye, sayarwa, mallaka, sufuri da kuma zubar da tarkacen ƙarafa da na’urorin lantarki.

A cewar sa, manufar dokar ita ce daƙile lalata kayayyakin gwamnati da na jama’a, kare muhalli, da kuma ƙarfafa tsaron jama’a.

Ya ƙara da cewa waɗannan ƙudirorin dokoki sun biyo bayan matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka a baya domin magance matsalar hauhawar kuɗin haya, yawan kuɗin dillalan gidaje, da kuma ayyukan masu kasuwancin tarkacen ƙarafa.

Omebeh ya ce zaman ya amince da miƙa ƙudirorin zuwa ga Majalisar Dokoki ta jihar domin yin dokar.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kafa lambunan magungunan gargajiya  (Herbal Heritage Gardens) mallakin jihar a yankunan sanatoci uku na Ebonyi.

Ya ce Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido ce za ta aiwatar da aikin tare da haɗin gwiwar Ma’aikatun Lafiya da Noma da Albarkatun Ƙasa, domin bunƙasa bincike, adanawa da kuma daidaita hanyoyin magungunan gargajiya na asali.

A cewar Omebeh, za a fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tantance wuraren da za a kafa cibiyoyin, da kuma tsara dokokin da za su jagoranci aikin nan take, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) da sauran cibiyoyin bincike masu ruwa da tsaki.

Ya ƙara da cewa cikin kwanaki 90 za a gabatar da wani ƙarin takarda ga majalisar da za ta ƙunshi dokokin da suka shafi daidaita ingancin magungunan gargajiya, kare haƙƙin mallakar fasaha, da kuma haɗa magungunan gargajiya cikin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

Majalisar Zartarwar ta kuma umurci Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a da ya fara aiwatar da matakan soke dukkan kwangilolin ayyukan titunan kilomita biyu da ba a kammala ba a faɗin jihar.

Omebeh ya ce an yanke wannan shawara ne bayan nazarin yadda ayyukan suka gudana, ya ƙara da cewa an kafa kwamitocin musamman na Majalisar Zartarwa a kowace ƙaramar hukuma domin tabbatar da kammala ayyukan kafin watan Satumba 2026.

Ya ce an kuma umurci Kwamishiniyar Ayyuka na Musamman, Dakta Misis Ngozi Obichukwu, da ta tattara jerin dukkan ayyukan titunan kilomita biyu da ba a kammala ba domin sauƙaƙa ɗaukar matakan da suka dace.

Bugu da ƙari, kwamishinan ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta amince da shirin zayyanawa, ginawa da kuma gudanar da masana’antar siminti mai ƙarfin samar da tan 6,000 a kowace rana (TPD) a Kamfanin Siminti na Nkalagu, cikin haɗin gwiwa da kamfanin Jiangsu Pengfei Group Ltd.

Ya ce aikin wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar na farfaɗo da harkokin masana’antu, jawo masu zuba jari, da kuma bunƙasa tattalin arzikin Jihar Ebonyi.

Tags: dokokiEbonyigwangwanhayar gidajeIkeuwah OmebehMajalisamasana'antusimintiƙarafa
Previous Post

CBN ya sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da daidaiton farashi, ya ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa

Next Post

‘Yan Majalisar Wakilai sun karɓi rahoton gyaran kundin tsarin mulki kan dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
‘Yan Majalisar Wakilai sun karɓi rahoton gyaran kundin tsarin mulki kan dokar kafa ‘yan sandan jihohi

'Yan Majalisar Wakilai sun karɓi rahoton gyaran kundin tsarin mulki kan dokar kafa 'yan sandan jihohi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!