Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa shirye-shirye da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu an shirya su ne ta yadda za su mori matasan Nijeriya, saboda gwamnati na amfani da sababbin dabaru wajen magance matsalolin zamani a wannan ƙarni na 21.
Ya yi wannan bayani ne a yau yayin ganawa da shugabannin ƙungiyar City Boy Movement a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, inda ya jaddada cewa gwamnati na ɗaukar matasa a matsayin ginshiƙin cigaban ƙasa da makomar dimokiraɗiyya.
Shettima ya ce gwamnatin Tinubu tana ɗaukar matakai masu wahala amma masu muhimmanci don farfaɗo da tattalin arziki da kuma tabbatar da cigaba mai ɗorewa, yana mai cewa samun nasarar gyare-gyare yana buƙatar haƙuri, jajircewa da goyon bayan ‘yan ƙasa.
Ya bayyana cewa dimokiraɗiyya ba ta tsaya kan zaɓe kaɗai ba, tana buƙatar shigar jama’a da kuma haɗin kai wajen kare manufofin da ke kawo cigaba ga ƙasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yaba wa kungiyar City Boy Movement bisa ƙoƙarin ta na wayar da kan jama’a da ƙarfafa goyon bayan gwamnati, yana mai jaddada muhimmancin ladabi, amana da haɗin kai a siyasa da shugabanci.
Ƙungiyar, wadda Hon. Francis Oluwatosin Shoga, yake jagoranta, ta yi alƙawarin ci gaba da zagayawa faɗin Nijeriya domin tattara goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027.







