Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ɗauki wasu sababbin matakan tsaro da nufin daƙile ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a faɗin jihar.
Daga cikin matakan akwai haramta sayarwa, saye, jigilar fetur da adana shi a cikin jarkoki, tare da rufe dukkan harkokin POS da wuraren cajin waya na kasuwanci a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Ibrahim Mohammed, ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a yau Talata.
Sanarwar ta ce an ɗauki waɗannan matakai ne a cikin wani Umarnin Zartarwa (Executive Order) da gwamnan ya bayar bayan wani taron gaggawa na tsaro da ya haɗa jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewar sanarwar, manufar sababbin matakan ita ce katse hanyoyin samar da kayan aiki da kuma hanyoyin sadarwa da ake zargin miyagun mutane suna amfani da su wajen aikata laifuffuka.
Sanarwar ta ce: “Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sanya hannu a kan wani sabon Umarnin Zartarwa domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar, musamman a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
“A ƙarƙashin wannan Umarni, an haramta sayarwa, saye, jigilar fetur da adana shi a cikin jarkoki a duk faɗin Jihar Katsina, kuma dokar ta fara aiki nan take. Wannan matakin an ɗauke shi ne domin hana fetur isa hannun miyagun mutane da ke buya a wurare masu nisa.
“Haka kuma, gwamnan ya amince da rufe dukkan cibiyoyin POS da wuraren cajin waya na kasuwanci a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa. Rahotannin tsaro sun nuna cewa wasu masu aikata laifi suna amfani da waɗannan wurare wajen gudanar da ayyukan su.”
Bugu da ƙari, an haramta amfani da babura a duk faɗin ƙananan hukumomin Matazu da Musawa. An ce wannan matakin zai kawo cikas ga zirga-zirga da ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, waɗanda galibi suke amfani da babura a matsayin hanyar sufuri.
Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar shi ne babban abin da gwamnatin sa ta sa a gaba, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan jihar.
Ya yi kira ga mazauna jihar da su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai ta hanyar bin waɗannan sababbin umarni tare da bayar da bayanan sirri masu amfani idan buƙatar hakan ta taso.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi sassauci ga duk wanda ya karya waɗannan dokoki ba, tana mai jaddada aniyar ta ta ɗaukar dukkan matakan da doka ta amince da su domin tabbatar da cewa al’ummomin jihar suna cikin tsaro, zaman lafiya da kuma yanayin da zai bunƙasa harkokin tattalin arziki da zamantakewa.







