Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Lahadi ya karɓi tikitin takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC domin zaɓen shekarar 2027, inda ya yi alƙawarin ƙarfafa sauye-sauyen da ake yi da kuma zurfafa cigaban ƙasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake gabatar da jawabin karɓar takara bayan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a babban zaɓen shekarar 2027.
Ya ce: “Yau, muna murnar wani muhimmin lokaci a tafiyar mu ta dimokiraɗiyya, tarihin da ba mutum guda ya gina ba, sai dai ƙudirin mu na bai-ɗaya.”
Shugaban Ƙasar ya tuna yadda ya zama ɗan takarar jam’iyyar a shekarar 2022 sannan daga bisani ya zama shugaban ƙasa da goyon bayan membobin jam’iyyar da ’yan Nijeriya.
“Yau, na dawo gare ku a matsayin shugaban ƙasa mai ci, cikin tawali’u saboda irin goyon bayan da kuka ci gaba da ba ni da kuma amincewar da kuka nuna,” inji shi.

Ya ƙara da cewa aikin da ke gaban jam’iyyar shi ne tabbatar da cigaba, ƙarfafa sauye-sauye da kuma shimfiɗa tubalin Nijeriya ta zamani.
Ya ce: “Na amince, cikin tawali’u da matuƙar godiya, da wannan tsayawar takarar da babbar jam’iyyar mu APC ta ba ni domin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.”
Haka kuma ya gode wa shugabannin jam’iyya, gwamnoni, Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ’yan majalisa da ‘ya’yan jam’iyyar bisa tabbatar da haɗin kai da ƙarfin da APC take da shi.
Shugaban ya kuma gode wa ’yan Nijeriya bisa goyon bayan abin da ya kira “hanya mai wahala amma mai muhimmanci ta sauye-sauye” da gwamnatin sa ta ɗauka.
Tinubu ya ce gwamnatin sa ta aiwatar da manyan sauye-sauyen tsari, ta ƙarfafa kuɗaɗen gwamnati tare da inganta tattara kuɗaɗen shiga ta hanyar sababbin manufofin haraji da kasafin kuɗi.
“Mun yi alƙawarin cire shingayen kuɗi da ke hana matasan mu samun ilimi mai zurfi. Yanzu mun kafa Asusun Lamunin Ilimi na Nijeriya,” inji shi.
A cewar sa, an riga an fitar da sama da Naira biliyan 282 ga fiye da mutum miliyan 1.5 da suka ci gajiyar shirin lamunin ɗalibai.
Game da sauye-sauyen wutar lantarki, Tinubu ya ce gwamnatin sa ta samar da mitocin wutar lantarki miliyan 2.5 tare da kafa shirin ‘bond’ na Naira tiriliyan 4 domin biyan tsofaffin basussukan da ake bin kamfanonin samar da wuta (GENCOs) da na iskar gas (GASCOs).
Ya ce: “A ƙarƙashin gwamnatin mu, samar da wutar lantarki ya kai wani lokaci megawatt 6,000, wanda ya fi abin da muka gada da kashi 50 cikin ɗari.”
Tinubu ya ce gwamnatin sa ta kuma cire tallafin man fetur, ta daidaita farashin canjin kuɗi tare da ƙaddamar da sauye-sauyen da za su ƙarfafa daidaiton tattalin arziki da amincewar masu zuba jari.
Shugaban ya ce gwamnatin sa ta bai wa ayyukan more rayuwa fifiko a ɓangarorin sufuri, wutar lantarki, gidaje, ban ruwa da haɗin sadarwar zamani domin bunƙasa cigaba mai amfani ga kowa da kuma masana’antu.
Ya ce: “Muna gina hanyoyi masu ɗorewa da manyan tituna a bakin teku da kuma hanyar Sakkwato zuwa Badagiri da za su iya ɗaukar sama da shekara 100.”
Tinubu ya yi la’akari da cewa har yanzu ’yan Nijeriya da dama suna fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa, amma ya tabbatar da cewa gwamnati tana mai da hankali wajen samar da mafita mai ɗorewa.
Shugaban ya kuma yi magana kan matsalar tsaro, inda ya tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa gwamnatin sa tana ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya tare da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa a faɗin ƙasar nan.
Ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta hanzarta yin gyaran kundin tsarin mulki domin ba da damar kafa ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar nan.
“Muna kuma sa ran Majalisar Dokoki ta yi gyaran kundin tsarin mulki domin kafa ’yan sandan jihohi a matsayin gaggawar ƙasa,” inji shi.
Shugaban ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa masana’antu, tabbatar da wadatar makamashi, wadatar abinci, cigaban more rayuwa da ƙarfafa dimokiraɗiyya.
Ya ce: “Manufar mu a bayyane take: gina Nijeriya inda rayuwar kowa za ta kasance cikin tsaro, inda harkokin kasuwanci za su bunƙasa, kuma matasa su samu damarmaki.”

Ya yi kira da a haɗa kai a ƙasa, tare da roƙon ’yan Nijeriya daga dukkan ɓangarorin siyasa, ƙabilu da yankuna da su yi aiki tare domin cigaban ƙasa.
Tinubu ya yi alƙawarin kafa gwamnati mai haɗa kowa da kowa tare da ci gaba da yi wa ’yan Nijeriya hidima cikin gaskiya, jajircewa da sabon ƙudiri.
“Na yi alƙawarin kafa gwamnati mafi haɗa kai, wadda za ta saurara, ta koya, kuma ta jagoranta bisa muradun dukkan ’yan Nijeriya,” inji shugaban.
A zaɓen fidda gwanin dai Tinubu ya samu ƙuri’u 10,999,162 domin lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a babban zaɓen shekarar 2027, bayan ya doke abokin hamayyar sa guda ɗaya, Stanley Osifo, a zaɓen fidda gwani na kai-tsaye da jam’iyyar ta gudanar a faɗin ƙasar nan.







