• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Wakilin Mu by Wakilin Mu
May 23, 2026
in Labarai
A A
0
Ana shirya wa alhazan Nijeriya bita kafin lokacin hawan Arafa

Ana shirya wa alhazan Nijeriya bita kafin lokacin hawan Arafa

An samu wata gagarumar nasara a harkokin aikin Hajjin bana yayin da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta kammala jigilar alhazan Nijeriya zuwa Saudiyya, inda aka yi jigilar alhazai sama da 40,000 cikin kwana 18 kacal.

Wannan nasara ta sake tabbatar da irin kulawa da muhimmancin da gwamnatin Tinubu take bai wa harkokin addini da jin daɗin al’ummar Nijeriya, musamman Musulmai masu gudanar da ibadar Hajji.

A cewar NAHCON, an gudanar da jimillar jirage 98 daga ranar 3 ga watan Mayu zuwa ranar 21 ga Mayu, inda aka yi jigilar alhazai 40,250 da suka samu bizar Hajji ta hannun hukumar. Wannan ya nuna irin ingantaccen shiri da tsare-tsaren da aka yi tun kafin fara aikin.

Shugaban NAHCON, Ambassador Isma’il Abba Yusuf, ya bayyana cewa nasarar da aka samu ba za ta rasa nasaba da cikakken goyon baya da jagorancin Shugaba Tinubu da kuma sa ido na kusa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, waɗanda suka tabbatar da samar da yanayin da ya ba da damar gudanar da aikin cikin sauƙi duk da ƙalubalen da ake fuskanta a duniya.

Haka kuma, kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa ya yaba da yadda aka gudanar da aikin Hajjin, inda ya bayyana cewa an samu gagarumin cigaba a fannin daidaitawa, haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma ingancin ayyukan da aka samar wa alhazai idan aka kwatanta su da na shekarun baya.

Yayin wata ziyarar sa ido da suka kai birnin Madina domin duba masaukan alhazai da tantance ayyukan da ake gudanarwa, shugaban tawagar, Sanata Ali Ndume, ya ce aikin Hajjin 2026 ya nuna kyakkyawan tsari, ingantaccen shugabanci da kuma ƙwarewar gudanarwa daga NAHCON da sauran hukumomin da ke da alhakin aikin.

Sanata Ali Ndume (a tsakiya) yana duba masaukin alhazai a Madina

Ya ƙara da cewa nasarar kammala jigilar alhazai kafin rufe sararin samaniyar Saudiyya wata shaida ce ta ingantaccen shiri da kuma kyakkyawan jagoranci wajen tabbatar da nasarar manyan ayyukan ƙasa.

Har ila yau, gwamnatin ta tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen gudanar da ayyukan Masha’ir a Mina, Arafat da Muzdalifah domin tabbatar da jin daɗi, tsaro da walwalar alhazan Nijeriya yayin gudanar da manyan rukunnan Hajji.

Wannan cigaba ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu take ƙara mayar da hankali wajen inganta ayyukan sufuri, gudanarwa da hidimomin jama’a, lamarin da ke haifar da sakamako mai kyau a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.

Bugu da ƙari, NAHCON ta ba da sanarwar cewa shirye-shiryen dawo da alhazai gida bayan kammala aikin Hajji sun riga sun fara, inda ake sa ran fara jigilar dawowa Nijeriya daga ranar 3 ga Yuni.

Yayin da miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban na duniya suke gudanar da wannan babban rukuni na Musulunci, Nijeriya ta sake nuna cewa tana da ƙwarewa da tsari wajen kula da alhazan ta, abin da ke ƙara ɗaga martabar ƙasar a idon duniya.

Ana sa ran wannan nasara za ta zama tubalin da za a gina sababbin nasarori a kai, musamman yayin da NAHCON ta ba da sanarwar cewa shirye-shiryen Hajjin shekarar 2027 za su fara nan take bayan kammala aikin Hajjin bana.

Previous Post

Zaɓen fidda gwanin APC ƙwarin gwiwar ɗorewar dimokiraɗiyya ne, inji Tinubu 

Next Post

2027: Tinubu ya zama ɗan takarar APC tare da alƙawarin ƙarfafa sauye-sauye

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
2027: Tinubu ya zama ɗan takarar APC tare da alƙawarin ƙarfafa sauye-sauye

2027: Tinubu ya zama ɗan takarar APC tare da alƙawarin ƙarfafa sauye-sauye

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!