Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, tare da Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwanaki uku a Amurka
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar ƙara zurfafa hadin gwiwa a fannin tsaro, yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afrika.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Asabar.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, ya kai ziyarar aiki ta kwanaki uku a Amurka, inda ya gana da manyan ƙusoshin gwamnatin ƙasar.
A yayin ziyarar, Ribaɗu ya isar da saƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jajircewa wajen ɗorewar dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Ribaɗu ya gana da Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, da sauran manyan jami’an diflomasiyya da na tsaro na Amurka.
Babban maƙasudin wannan ganawa shi ne duba yadda za a inganta raba bayanan sirri da kuma ƙarfafa ayyukan soji na haɗin gwiwa.
Ribaɗu ya jaddada muhimmancin taimakon juna don magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin Sahel, musamman Ayyukan ta’addanci da tsageranci, safarar miyagun ƙwayoyi da makamai da laifukan da ake aikatawa ta hanyar yanar gizo.
Hukumomin Amurka sun jinjina wa Nijeriya a matsayin ta na jagora a yankin Afrika, musamman wajen jagorantar yaƙi da ta’addanci a tafkin Chadi.
A nata ɓangaren, Nijeriya ta bayyana cewa tana amfani da dabarun ƙarfin soja da kuma tattaunawa da inganta rayuwar jama’a don magance tushen matsalar rashin tsaro.
“Nijeriya tana godiya ga Amurka bisa taimakon da take bayarwa a ɓangaren horar da jami’ai, ba da bayanan sirri, da kuma tallafin jinkai,” inji Ribaɗu.
A ƙarshen taron, ɓangarorin biyu sun amince su ci gaba da tuntuɓar juna a kai a kai ta hanyar haɗin gwiwa na musamman don tabbatar da cewa dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla sun fara aiki yadda ya kamata.







