Wani babban jami’in Sojojin Nijeriya da ba a bayyana sunan sa ba tare da wasu sojoji shida sun mutu a daren jiya bayan motar su ta taka wani bam ɗin ƙasa (IED) da ’yan ta’adda suka dasa a Monguno, Jihar Borno.
Jami’in yaɗa labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa (Arewa maso Gabas), Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Litinin cewa lamarin ya faru ne bayan dakarun da ke ƙarƙashin Sashen 3 na Rundunar Haɗin Gwiwa (Arewa maso Gabas), a ƙarƙashin Operation Haɗin Kai, sun fuskanci wani harin ’yan ta’adda na Tango a wani wuri mai suna Charlie 13 a Monguno, a daren Lahadi, 12 ga Afrilu.
Ya ce: “Bayan musayar wuta mai tsanani, an fatattaki ’yan ta’addan, inda dakarun suka ci gaba da riƙe ikon yankin.
“Abin takaici, kwamandan rundunar, yayin da yake cikin jarumtaka yana kan hanyar sa ta zuwa wurin dakarun domin duba halin da ake ciki da kan sa, ya gamu da wani bam ɗin IED wanda ya lalata motar sa matuƙa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sa tare da wasu jaruman sojoji shida.
“Ayyukan sa, ko bayan an shawo kan barazanar farko, sun nuna mafi girman halayen shugabancin soja; jarumtaka, sadaukar da kai ba tare da son kai ba, da jagoranci daga gaba.
“Ƙudirin sa na tunkarar dakarun a tsakiyar faɗa duk da haɗarin da ke akwai, ya zama babbar shaida ta jarumtaka, nauyin da ke kan sa, da kuma jajircewar sa wajen tabbatar da walwala da ingancin ayyukan dakarun sa.”
Uba ya ƙara da cewa: “Operation HAƊIN KAI na matuƙar alhinin rashin wannan fitaccen jami’i da sauran jaruman da suka biya mafi girman farashi wajen hidimta wa ƙasa.
“Sadaukarwar su za ta kasance a zukatan Rundunar Sojin Ƙasa da kuma al’ummar ƙasar da suka yi wa hidima har abada.”






