• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN zai sake ƙarfafa jarin Cibiyoyin Bunƙasa Tattalin Arziki (DFIs) don bunƙasa ƙanana da matsakaitan masana’antu

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 13, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Bankin CBN

Bankin CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) yana yunƙurin sake ƙarfafa jari da kuma sake fasalin cibiyoyin bayar da kuɗin bunƙasa tattalin arziki domin magance babban gibin kuɗaɗe da ke fuskantar matsakaita da ƙananan kamfanoni (MSMEs).

Yiwuwar wannan gagarumin aikin ya fito ne daga bakin Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da manufofin tattalin arziki, Muhammad Abdullahi, inda ya bayyana hakan a wani zaman tattaunawa yayin ƙaddamar da rahoton Bankin Duniya kan Nijeriya.

Tun a makon jiya ne dai aka gudanar da taron a Abuja, inda ya ce wani bincike da CBN ya gudanar kwanan nan ya nuna cewa cibiyoyin DFIs da ake da su ba su da sukunin biyan bukatun bayar da rance ga kamfanoni.

“Mun gudanar da wata bita a bara a fannin bayar da kuɗin bunƙasa hadahada. Idan aka tattara dukkan DFIs a Nijeriya, jimillar kadarorin su ta dan fi Naira tiriliyan 8 kadan, alhali abin da ake buƙata don MSMEs, ana so ya haura Naira tiriliyan 130,” inji shi.

Abdullahi ya bayyana cewa wannan babban gibi tsakanin abin da ake da shi da abin da ake buƙata na nuna bukatar gaggawar yin gyare-gyare a fannin, ba wai ƙara jari kaɗai ba.

“Hanya ɗaya tilo ta magance wannan ba wai saka jari daga gwamnati kaɗai ba ne, har ma da sanya waɗannan cibiyoyi su zama masu jan hankalin masu zuba jari da kuma masu iya samun riba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa CBN tare da Ma’aikatar Kuɗi sun riga sun fara duba tsarin DFIs domin inganta aikin su, ciki har da tsarin ƙarfafa gwiwa da kuma yadda suke amfani da jari yadda ya kamata.

“Muna duba dukkan tsarin domin mu gyara ƙarfafawa, mu inganta sha’awar ɗaukar kalubale sannan mu ƙara ƙarfin jarin su,” inji shi.

Ya ce gyaran zai shigar da ƙa’idojin kasuwa sosai cikin ayyukan DFIs.

“Muna nazarin tsarin domin ganin yadda za a ƙara amfani da ƙa’idojin kasuwa, domin yadda ake yi a baya bai kawo sakamakon da ake so ba,” ya ce.

Abdullahi ya jaddada cewa samun damar kuɗi ga matsakaita da ƙananan kamfanoni har yanzu babban ƙalubale ne a tsarin tattalin arzikin Nijeriya, musamman ga MSMEs.

“Ba da rance ya daɗe yana daga cikin manyan ƙalubale wajen tabbatar da cewa kuɗi ya kai ga kamfanonin da suke buƙata,” inji shi.

Ya kuma nuna cewa ƙoƙarin sake ƙarfafa jarin bankuna da aka yi kwanan nan zai taimaka wajen ƙara ƙarfin su na bayar da rance.

Tags: CBNkamfanonimasana'antuMuhammad AbdullahiOlayemi Cardoso
Previous Post

Tinubu ya umurci jami’an gwamnatin sa da su nemo hanyoyin rage raɗaɗin tsadar rayuwa

Next Post

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!