• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Jam’iyyar ADC ba ta rubuto takardar neman izinin yin babban taron ta a Dandalin Eagle ba, inji Wike

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
April 13, 2026
in Siyasa
A A
0
Jam’iyyar ADC ba ta rubuto takardar neman izinin yin babban taron ta a Dandalin Eagle ba, inji Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya, Mista Nyesom Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Mista Nyesom Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Mista Nyesom Wike, ya yi watsi da zargin cewa wai an hana jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) amfani da filin Dandalin Eagle domin gudanar da babban taron ta na ƙasa.

Wike, wanda ya bayyana hakan a yau Litinin bayan ya duba ayyukan da ake yi a Abuja, ya bayyana zargin a matsayin “maras tushe”, yana mai cewa babu wata takardar neman izini da aka gabatar a hukumance don amfani da wurin.

Jam’iyyar ADC ta nuna damuwa kan matsalolin samun wurin da za ta gudanar da babban taron ta na ƙasa, wanda aka shirya yi a gobe Talata a Abuja.

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na taron jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, shi ne ya bayyana hakan a yau Litinin.

Ologbondiyan ya ce har zuwa ƙasa da sa’o’i 24 kafin taron, jam’iyyar ba ta samu amincewa da wani wuri ba.

Ministan ya ce: “Wa ya hana su? Ban san da wani irin abu haka ba.

“Idan African Democratic Congress ce, to irin wannan zargi nasu ne na yau da kullum don neman tausayi daga jama’a.”

Ya bayyana cewa amfani da Dandalin Eagle yana buƙatar bin ƙa’ida, wanda ya haɗa da gabatar da takardar nema ta hanyar kamfanin Abuja Investments Company Ltd, wanda ke kula da wurin, tare da biyan kuɗaɗen da suka dace.

Ministan ya kuma nuna cewa Velodrome na Dandalin Wasanni na Moshood Abiola na Ƙasa ba ya ƙarƙashin ikon Hukumar FCT, sai dai na Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa.

Ya ce:“Yanzu haka, babu wata takardar nema da aka gabatar ga Abuja Investments Company Ltd.

“Lokacin da jam’iyyar APC ta yi amfani da wurin, haka kuma PDP ta yi amfani da Velodrome na filin wasan, sun bi dukkan matakan da aka tanada.

“Ba mu hana kowa amfani da wurin idan an bi ƙa’idoji,” inji shi.

Da yake magana kan ayyukan da ya duba, ministan ya nuna gamsuwa da yadda aikin ke tafiya, yana mai tabbatar da cewa manyan ayyukan tituna za su kammala kafin ranar 15 ga Mayu.

“’Yan kwangila sun tabbatar mana cewa za a kammala ayyukan tituna kafin 15 ga Mayu, yayin da aiki n shigar da fitilun titi za a kammala shi kafin ƙarshen watan Mayu,” inji shi.

A unguwar Gaduwa, Wike ya ce ya umurci a saka shinge na kariya domin hana mamaye hanyoyin tituna, yayin da aikin fitilun titi yake ci gaba.

A unguwar Wassa kuma, ministan ya bayyana cewa gwamnatin FCT tana shirin tada masu sana’a da ‘yan kasuwar kayan gyaran mota da ke aiki a Apo Mechanic a kan hanyar Outer Southern Expressway.

Ya ce za a mayar da su wani sabon wuri da aka tanada da kayan more rayuwa da suka dace.

“Manufar wannan shirin shi ne inganta yanayin aikin masu sana’a tare da cika alƙawurran da aka daɗe ana yi wa ɓangaren tattalin arzikin da ba na gwamnati ba,” inji shi.

Wike ya danganta cigaban ayyukan FCT da haɗin kai mai kyau tsakanin gwamnati da ‘yan kwangila, tare da biyan kuɗaɗen kwangila a kan lokaci.

Tags: ADCAPCEagle SquareNyesom WikePDPZaɓen2027
Previous Post

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

Next Post

Sarkin Kano ya halarci taron daraktocin MTN a Afrika ta Kudu

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Sarkin Kano ya halarci taron daraktocin MTN a Afrika ta Kudu

Sarkin Kano ya halarci taron daraktocin MTN a Afrika ta Kudu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!