• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fito da sababbin sauye-sauye a tsarin biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani, har ya kafa wa tsarin kwamiti

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 4, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Gwamnan CBN, Mista Olayemi Cardoso

Gwamnan CBN, Mista Olayemi Cardoso

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kafa Kwamitin Kamfanonin Fasahar Hadahadar Biyan Kuɗi na Zamani (PSPC), wato Payment Service Providers Committee, a matsayin wani ɓangare na sabon ƙudirin sa na ƙarfafa dokoki a wannan fanni, tare da hanzarta sauye-sauye, inganta haɗin kai, da kuma magance matsalolin da ke addabar harkar hadahadar kuɗi ta zamani.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, shi ne ya ƙaddamar da kwamitin a taron farko da aka yi a Lagos a makon nan.

Daga cikin manyan ayyukan kwamitin shi ne tsara sabuwar manufa ta tsarin biyan kuɗi. Haka kuma kwamitin ya haɗa da CBN, da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Hukumar Kariya ga Masu Ajiya (NDIC), da Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC), da kuma Nigeria Inter-Bank Settlement System Plc (NIBSS).

Wannan ya nuna fara wani tsari mai ƙarfi na haɗin gwiwar hukumomi kan batutuwan da suka shafi tsarin biyan kuɗi a Nijeriya.

Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da bangaren Manufofin Tattalin Arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin ƙarfafa daidaiton manufofi, zurfafa musayar ilimi, da kuma sauƙaƙa warware matsaloli tare a wani fanni da ke ƙara zama ginshiƙi ga bunƙasar tattalin arziki.

Ya ce CBN na shirin ƙaddamar da sabuwar manufa ta tsarin biyan kuɗi, wadda za ta tsara makomar tsarin kuɗaɗen dijital na Nijeriya cikin shekaru uku masu zuwa.

Abdullahi ya ce: “A cikin ’yan shekarun nan, tsarin biyan kuɗi ta hanyar dijital a Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba.

A shekarar 2024 kaɗai, an gudanar da sama da biliyan 11.2 na ma’amaloli ta hanyoyin zamani, wanda adadin kuɗin ya kai sama da naira tiriliyan dubu, wato ‘quadrillion’ 1.07 kenan.

Wannan shi ne karo na farko da biyan kuɗi ta dijital ya wuce wannan mataki, wanda ke nuna babban ci gaba.

“Wannan ci gaba ya ƙara habaka ne a 2025, haka kuma a watannin farko na 2026. Wannan fanni yana bunƙasa sosai, kuma yana da tasiri mai girma ga tattalin arzikin Nijeriya da haɓakar da ya haɗa kowa da kowa da kasuwanci da sauran alfanun ƙasa.

“Saboda haka ya zama dole CBN ya ƙaddamar da wannan kwamiti domin ƙarfafa haɗin kai a manufofi, musayar ilimi, da kuma tabbatar da warware matsaloli tare tsakanin masana’antu da Babban Banki.”

Ya ƙara da cewa kafin kafa kwamitin, hulɗa tsakanin masu gudanar da harkokin hadahadar kudade da masu tsara dokoki tana yawan zama rarrabe, kuma hakan kan jinkirta magance matsaloli. Sabon tsarin, a cewar sa, zai taimaka wajen saurin warware matsaloli da kuma samar da manufofi cikin sauri.

Dangane da sabuwar manufa, ya ce: “Cikin kusan wata guda daga yanzu, za mu ƙaddamar da sabuwar manufa ta tsarin biyan kuɗi wadda za ta fayyace inda muke son tsarin ya dosa cikin shekaru uku masu zuwa. An tsara wannan manufa tare da haɗin gwiwar kamfanonin fasahar kuɗi, masu gudanar da kuɗin wayar hannu, da masu ba da sabis na biyan kuɗi.”

Mataimakin Gwamna mai kula da Tsaron Tsarin Kuɗi, Philip Ikeazor, ya ce za a aiwatar da sabbin manufofi na kai-tsaye don yaƙi da halasta kuɗin haram da kuma damfara a bankuna da masu ba da sabis na biyan kuɗi domin ƙarfafa tsaro.

Ya ce: “Dangane da rage haɗarin damfara, mun ga cewa yawan damfara ya ragu da kashi 50 tsakanin 2024 da 2025. Mun kuma fito da sabuwar manufa ta atomatik don yaƙi da halasta kuɗin haram da damfara, wadda za ta taimaka matuƙa wajen rage irin waɗannan laifuka idan aka aiwatar da ita a bankuna da masu ba da sabis na biyan kuɗi.”

Har ila yau, Manajan Darakta na NIBSS, Premier Oiwoh, ya yaba wa CBN bisa wannan mataki, yana mai cewa hakan zai ƙara bunƙasa tsarin biyan kuɗi a ƙasar.

Daga ɓangaren masana’antu kuma, Shugabar EFInA, Foyinsolami Akinjayeju, ta ce: “Mun samu gagarumin ci gaba a haɗa jama’a cikin harkar kuɗi sakamakon kirkire-kirkire daga masu ba da sabis na kuɗi da ba bankuna ba, musamman a fannin biyan kuɗi. Don haka rawar da masu ba da sabis na biyan kuɗi za su taka wajen ƙarfafa ci gaban da ya haɗa kowa na da matuƙar muhimmanci. Wannan dandali mataki ne mai kyau domin samar da mafita cikin gaggawa ga matsalolin da ke damun tsarin biyan kuɗi a Nijeriya.”

Tags: bankunaCBNOlayemiCardoso
Previous Post

Ku jaruman gaske ne na ƙasar mu, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta faɗa wa ‘yan wasa a taron kammala Gasar Naƙasassu ta Ƙasa karo na 3

Next Post

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!