• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamna Lawal Dare ya yi murnar saukar jirkin sama na farko a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau… Lahadi

ALI KANO by ALI KANO
March 23, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamna Lawal Dare ya yi murnar saukar jirkin sama na farko a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau… Lahadi
Jirgin Bombardier Challenger 605 jim kaɗan bayan saukar sa a matsayin jirgin gwaji na farko a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau, a Gusau, Jihar Zamfara, ranar Lahadi.

Jirgin Bombardier Challenger 605 jim kaɗan bayan saukar sa a matsayin jirgin gwaji na farko a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau, a Gusau, Jihar Zamfara, ranar Lahadi.

Gwamna Dauda Lawal Dare a ranar Lahadi ya bayyana matuƙar farin cikin sa kan saukar jirgi ta abar tarihi da aka gudanar a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau.

Wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ta bayyana cewa jirgin gwajin ya sauka a filin jirgin da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce Gwamnatin Tarayya ce ta sarrafa jirgin, ƙirar Bombardier Challenger 605.

Wani ɓangare na sanarwar ya ce, “Yau za ta kasance rana ta tarihi a tarihin Zamfara, yayin da Gwamna Lawal ya shaida saukar jirgi na farko a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau.

“Jirgin, mai lambar rajista 5N-FGZ, ya gudanar da saukar gwaji ta musamman domin tantance ƙarfin filin jirgin wajen karɓar manyan baƙi (VIP) da aka shirya a mako mai zuwa.

“An gudanar da gwajin jirgin ne bisa tanade-tanaden Dokokin Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya (Nig. CARs) Sashe na 12.1.4.1(c).”

A cewar sanarwar, kafin gwajin jirgin, gwamnatin jihar ta nemi izini daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), kuma hukumar ta ba da izinin musamman na sauka ba tare da wata matsala ta fasaha ba (No Technical Objection – NTO) domin jirgin ya sauka a Gusau.

“An gudanar da aikin jirgin ne bisa ƙa’idar Visual Flight Rules (VFR), wadda ke gudana ne daga fitowar rana zuwa faɗuwar ta kawai.

“Wannan gwajin jirgi na tarihi ya ƙara ɗaga martabar gwamnatin Gwamna Lawal, musamman ganin cewa Zamfara ba ta da filin jirgin sama tsawon sama da shekaru 30.

“Gwamnatin Zamfara, ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal, na gina filin jirgin, kuma ana sa ran fara ayyukan sa nan da watan Maris 2026,” inji sanarwar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa aikin wannan filin jirgin na zamani ya haɗa da titin sauka da tashi, ginin tashar fasinjoji, da hasumiyar kula da zirga-zirgar jirage, waɗanda ake sa ran za su ƙarfafa harkokin tattalin arziki da jawo zuba jari a jihar.

NAN ya tunatar da cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, tare da Gwamna Dauda Lawal, a ranar 21 ga Yuni, 2024, suka ƙaddamar da aikin gina Babban Filin Jirgin Sama na Ɗaukar Kaya.

Tags: filin jirgiGusausaukar gwaji
Previous Post

Ba za mu bari rashin tsaro ya dusashe ƙoƙarin da muke na taimaka wa marasa ƙarfi ba — Tinubu

Next Post

ICPC za ta gurfanar da El-Rufai a kotu a Kaduna gobe Talata

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i

ICPC za ta gurfanar da El-Rufai a kotu a Kaduna gobe Talata

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!