Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka masu Alaƙa (ICPC) ta bayyana cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, a kotu gobe Talata.
El-Rufa’i dai yana tsare ne tun bayan da ya amsa gayyatar Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a ranar 16 ga Fabrairu, 2026.
EFCC ta yi masa tambayoyi na tsawon awanni 48 kafin daga bisani ICPC ta karɓe shi zuwa hannun ta.
Tsare shi na tsawon lokaci ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda ƙungiyoyi da mutane da dama suka buƙaci a gurfanar da shi a kotu ko kuma a sake shi.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun ICPC, Mista John Okor Odey, ya ce za a gurfanar da El-Rufa’i ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna a ranar Talata.
“Shari’ar, mai lamba FHC/KD/73/2026, tana ɗauke da tuhume-tuhume da suka haɗa da karkatar da dukiyar jama’a da mallakar kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, zuwa safarar kuɗaɗe ta haram.
“Haka kuma, an shigar da wata ƙarar mai lamba KDH/KAD/ICPC/01/26, a kan Malam Nasir El-Rufa’i da wani Amadu Sule (LEDA), a Babbar Kotun Jihar Kaduna a ɓangaren shari’a na Kaduna.
“Tuhume-tuhumen da ke cikin ƙarar kotun jiha sun haɗa da cin zarafin ofis, zamba, yunƙurin aikata zamba, da bai wa wani gata ba bisa ƙa’ida ka’ida ba, da sauran su.
“Dukkanin ƙarar ICPC ta shigar da su ne a ranar 18 ga Maris, 2026.
“Za a faɗi ranar gurfanarwa a kotun jiha a lokacin da kotu ta tantance.”
ICPC ta ce an riga an miƙa wa El-Rufa’i takardun ƙarar yadda ya dace.







