• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Ba za mu bari rashin tsaro ya dusashe ƙoƙarin da muke na taimaka wa marasa ƙarfi ba — Tinubu

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
March 22, 2026
in Tsaro
A A
0
Ba za mu bari rashin tsaro ya dusashe ƙoƙarin da muke na taimaka wa marasa ƙarfi ba — Tinubu
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da gwamnonin jihohi a lokacin ziyarar a Legas

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da gwamnonin jihohi a lokacin ziyarar a Legas

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya ce gwamnatin sa za ta ƙara ƙaimi wajen tunkarar ƙalubalen rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, tare da tabbatar da cewa tsaro da walwalar ‘yan ƙasa suna cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a tarurrukan da aka yi a Birtaniya.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa Shugaban Ƙasar, wanda ya karɓi baƙuncin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da gwamnoni 23 a gidan sa da ke Legas domin bikin Eid el-Fitr a yau Lahadi, ya ce ya ci gaba da tuntuɓar Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, kan tallafi da kayan aikin tsaro na zamani.

Ya ce: “Kasancewar ku a nan yau da kuma yawan ku yana nuna gaskiyar ku, jajircewar ku da kuma darajar zumunci da haɗin kai.

“Mataki na gaba na gwagwarmayar mu yana gab da mu, kuma shi ne ƙalubalen rashin tsaro a ƙasar nan.

“Ina yin dukkan ƙoƙari domin mu samu farin cikin nasarar da muka samu kan zalunci gaba ɗaya. Rashin tsaro maƙiyi ne na cigaba, bunƙasa da wadata. Ina farin cikin cewa dukkan ku kuna sane da wannan ƙalubale.

“Ni a ɓangare na, na ƙudiri aniyar ƙara ƙarfafa hulɗa da hanyoyin sadarwa da ake buƙata. Ɗaya daga cikin muhimman tattaunawa da muka yi a Birtaniya shi ne kan kayan aiki da tallafi.

“Zan iya sanar da ku cewa jiya ma na sake yin doguwar tattaunawa da Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Suna haɗa kai da mu wajen samar da kayan aiki da tallafi. Haka kuma ina ƙoƙarin tuntuɓar wasu ƙasashe,” inji shi.

Shugaban Ƙasa kasa tare da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, sun dawo ranar Juma’a daga ziyarar kwana uku a Birtaniya, inda Sarki Charles na III da Sarauniya Camila suka karɓe su.

Haka kuma Shugaban Ƙasar ya gana da Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, kafin dawowar sa Nijeriya domin bikin Ƙaramar Sallah.

Ya ce: “Ya kamata mu fi kula da masu rauni. Na san rikicin Gabas ta Tsakiya zai ƙara hauhawar farashi kuma zai shafi ƙarfin sayen mu. Ƙungiyoyin ƙwadago da sauran su za su ƙara matsa lamba kan mu ba da ƙarin tallafi sakamakon wannan rikici.”

Shugaban Ƙasar ya buƙaci gwamnoni da su ci gaba da jajircewa da kuma nuna ƙarko wajen mayar da manufofi da hangen nesan su zuwa tsare-tsare da shirye-shiryen da za su yi tasiri kai-tsaye ga rayuwar ‘yan ƙasa, tare da goyon bayan gwamnati wajen yaƙi da “zaluncin” masu aikata laifi.

Tinubu ya shawarci gwamnoni da su samar da ƙarin tallafi domin rage raɗaɗin hauhawar farashin makamashi da sufuri sakamakon yaƙin Gabas ta Tsakiya.

Ya kuma gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bisa ziyarar jaje da ya kai Jihar Borno, tare da tabbatar wa da al’ummar jihar da ƙarin tsaro ta hanyar amfani da sababbin fasahohi.

A nasa ɓangaren, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa tsoma bakin sa a jihohi ta hanyar shirin “Renewed Hope Agenda”.

Ya ce: “A madadin abokan aiki na gwamnoni, muna miƙa saƙon gaisuwar wannan lokaci daga al’ummar jihohin mu daban-daban. Muna gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa rahamar sa da ta kai mu ga ganin ƙarshen watan Ramadan.

“Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya kai mu ƙarshen lokacin azumi (Lent), kuma ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa.”

Shugaban ya taya Shugaban Ƙasa murnar nasarar ziyarar aiki zuwa Birtaniya da kuma yarjejeniyoyin zuba jari da aka cimma.

“Yayin da manufar mu ita ce samar da kyakkyawar alaƙa da Birtaniya, wannan ziyarar aiki — ta farko cikin shekaru 37 — babba ce kuma mai muhimmanci. Tana nuna sabon matakin dangantaka da Nijeriya, kuma muna gode maku.

“Dole ne mu haɗa kai wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro. Dangane da ‘yan sandan jihohi, ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin tsaro ƙarƙashin jagorancin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaron Ƙasa, kuma NGF ta bayar da gudunmawar ta.

“NGF za ta miƙa takardar zuwa Majalisar Tarayya domin samar da tsarin doka na ‘yan sandan jihohi.”

Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Sanata Hope Uzodinma na Jihar Imo; Alex Otti na Jihar Abiya; Umo Eno na Jihar Akwa Ibom; Douye Diri na Jihar Bayelsa; Hyacinth Alia na Jihar Binuwai; Bassey Otu na Jihar Kuros Riba; Sheriff Oborevwori na Jihar Delta; Francis Nwifuru na Jihar Ebonyi; Monday Okpebholo na Jihar Edo; Peter Mbah na Jihar Inugu; Mohammed Inuwa Yahaya na Jihar Gombe; da Umar Namadi na Jihar Jigawa.

Sauran sun haɗa da Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano; Dikko Umaru Raɗɗa na Jihar Katsina; Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi; Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas; Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa; Caleb Mufwang na Jihar Filato; Siminalayi Fubara na Jihar Ribas; Agbu Keffas na Jihar Taraba; Mai Mala Buni na Jihar Yobe; da Lucky Aiyedatiwa na Jihar Ondo.

Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, shi ma ya halarci taron.

Tags: BirtaniyaBolaTinubugwamnoniNGFSallahSarkiCharlesIIItsaroziyara
Previous Post

Kano ta samu cibiyoyin sauya motoci zuwa CNG guda 41 yayin da Gwamnatin Tarayya take ƙara faɗaɗa shirin

Next Post

Gwamna Lawal Dare ya yi murnar saukar jirkin sama na farko a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau… Lahadi

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Next Post
Gwamna Lawal Dare ya yi murnar saukar jirkin sama na farko a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau… Lahadi

Gwamna Lawal Dare ya yi murnar saukar jirkin sama na farko a Babban Filin Jirgin Sama na Gusau... Lahadi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!