• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Maiduguri: Mutum 23 suka rasu, 146 suka jikkata, yayin da sojoji na gargaɗin akwai ‘yan harin ƙunar baƙin wake da dama a Borno

ALI KANO by ALI KANO
March 17, 2026
in Tsaro
A A
0
Maiduguri: Mutum 23 suka rasu, 146 suka jikkata, yayin da sojoji na gargaɗin akwai ‘yan harin ƙunar baƙin wake da dama a Borno
Wani soja a ɗaya daga cikin wuraren da bama-bamai suka halaka jama'a a Maiduguri

Wani soja a ɗaya daga cikin wuraren da bama-bamai suka halaka jama'a a Maiduguri

Mazauna Maiduguri sun shiga alhini da firgici bayan wasu jerin fashe-fashe da aka tsara suka girgiza muhimman wurare a birnin a daren Litinin, inda aƙalla mutane 23 suka mutu, yayin da 146 suka jikkata.

Ana zargin cewa hare-haren na hannun wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, kuma sun kai farmaki ne a wuraren taruwar jama’a a lokacin yammacin da mutane ke yawan zirga-zirga, daidai lokacin buɗe-baki (Iftar) da Musulmai ke kai azumi.

Hukumomin ‘yan sanda sun tabbatar da cewa fashe-fashen sun faru da misalin ƙarfe 7:24 na yamma a manyan wurare uku: kasuwar Monday mai cike da jama’a, ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, da gadar sama ta Post Office.

A wata sanarwa da aka fitar a yau Talata, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno, Nahum Kenneth-Daso, ya ce lamarin na da alaƙa da hare-haren ƙunar baƙin wake da ake zargi.

“Abin takaici, jimillar mutane ashirin da uku sun rasa ran su, yayin da sama da mutum ɗari suka samu raunuka iri-iri,” inji shi, yana mai ƙarawa da cewa adadin waɗanda suka jikkata ya ƙaru zuwa kusan 146 yayin da ake gano ƙarin waɗanda abin ya shafa da kuma kula da su.

Jami’an tsaro sun bayyana hare-haren a matsayin waɗanda aka tsara sosai, inda masu kai harin suka nufi wuraren da jama’a ke yawan taruwa domin haddasa ɓarna mai yawa.

Rundunar haɗin gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas, Operation Haɗin Kai, ta bayyana cewa bayanan sirri sun nuna yiwuwar shigar da masu harin ƙunar baƙin wake da dama cikin birnin.

A cewar kakakin ta, Laftanar Kanar Sanni Uba, maharan sun kai hare-haren ne a lokacin ƙololuwar zirga-zirga domin haddasa firgici da asarar rayuka mai yawa.

“Bayanan farko sun nuna cewa ‘yan ta’adda na iya shigar da masu harin ƙunar baƙin wake da dama cikin Maiduguri domin kai hare-hare a wuraren da jama’a suke taruwa,” inji shi.

Gargaɗin ya ƙara dagula fargabar yiwuwar ƙarin barazana a cikin birnin, wanda ya sa hukumomi suka ƙara tsaurara sa ido da kuma ayyukan gano abubuwan fashewa (IED).

Bayan faruwar fashe-fashen, wata haɗaɗɗiyar tawaga ta rundunonin ‘yan sanda, sojoji, da sauran hukumomin tsaro ta garzaya don tabbatar da tsaron wuraren da abin ya shafa.

Ƙwararru kan kawar da abubuwan fashewa (EOD) sun gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da cewa babu wasu na’urorin fashewa da aka bari a wuraren.

Masu ba da agajin gaggawa, ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a cikin birnin, ciki har da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, Babban Asibiti, da Asibitin Ƙwararru.

Ƙungiyoyin likitoci sun ci gaba da aiki dare da rana domin ceto rayukan waɗanda suka jikkata, da dama daga cikin su sun samu munanan raunuka.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Borno, CP Naziru Abdulmajid, ya ziyarci wuraren da fashe-fashen suka faru domin duba halin da ake ciki tare da kwantar da hankalin mazauna.

Ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada ƙudirin rundunar wajen dawo da tsaro.

Duk da cewa an samu ɗan sauƙin hali, hukumomin tsaro sun buƙaci mazauna da su yi taka-tsantsan, musamman su guji wuraren da jama’a ke taruwa a halin yanzu.

Haka kuma sun buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani motsi da ake zargi, abubuwan da aka bari babu kowa a kan su, ko wasu abubuwan da ba a saba gani ba cikin gaggawa.

“Muna roƙon jama’a da su kasance masu lura tare da haɗa kai da hukumomin tsaro yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran waɗanda ake zargi da kuma hana aukuwar karin hare-hare,” inji Uba.

Tags: bamBokoHaramharikisakisan gillaMaidugurita'addanci
Previous Post

Tinubu zai bar Abuja ranar Talata domin ziyarar tarihi ta ƙasa zuwa Birtaniya

Next Post

Harin Maiduguri: Tinubu ya tura manyan hafsoshi Borno don magance ta’addanci

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Harin Maiduguri: Tinubu ya tura manyan hafsoshi Borno don magance ta’addanci

Harin Maiduguri: Tinubu ya tura manyan hafsoshi Borno don magance ta’addanci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!