• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu zai bar Abuja ranar Talata domin ziyarar tarihi ta ƙasa zuwa Birtaniya

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
March 16, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu ya taya APC murnar nasara a zaɓuɓɓukan Birnin Tarayya, Kano da Ribas
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Bola Tinubu zai bar Abuja gobe Talata domin kai Ziyarar Ƙasa (State Visit) zuwa Birtaniya, bisa gayyatar Mai Martaba Sarki Charles na III da Sarauniya Camilla.

Shugaban ƙasar zai tafi tare da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, domin halartar muhimman ayyukan hukuma da aka tsara yayin ziyarar.

Sarki Charles na III zai karɓi baƙuncin Tinubu da Uwargidan sa a fadar Windsor Castle daga ranar Laraba zuwa Alhamis a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen ziyarar ƙasar.

Hakan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar yau Litinin a Abuja.

Wannan Ziyarar Ƙasa ita ce ta farko da wani shugaban Nijeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37, inda sarkin na Birtaniya zai karɓi baƙuncin sa a Windsor Castle.

Nijeriya da Birtaniya suna da tsayayyun dangantakar diflomasiyya da tarihi, waɗanda aka gina tsawon shekaru ta hanyar haɗin gwiwar siyasa, tattalin arziki da al’adu.

Ana sa ran wannan ziyara za ta ƙara ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu tare da buɗe sababbin hanyoyin haɗin gwiwa a tsakanin su.

Fannonin haɗin gwiwar da za a tattauna a kan su sun haɗa da shige-da-fice, kasuwanci, zuba jari da musayar al’adu.

Yayin da suke fadar Windsor Castle, Mai Martaba Sarkin da Sarauniyar za su gayyaci Shugaban Ƙasa da Uwargida Remi su duba baje-kolin kayayyakin fada na musamman daga Royal Collection waɗanda suka shafi Nijeriya.

Sarki da Shugaba Tinubu za su kuma gudanar da tattaunawar sirri, sannan su gana da ƙungiyoyi da ke aiki kan tattaunawar addinai daban-daban (interfaith dialogue) a matakin ƙasa da na duniya.

Daga baya, Iyalan Sarauta za su shirya liyafar cin abinci ta ƙasa (State Banquet) domin girmama baƙin daga Nijeriya.

Haka kuma, Tinubu zai yi ganawar biyu-da-biyu da Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, gidan sa da ke lamba 10 Downing Street.

Ana sa ran ganawar za ta ƙara ƙarfafa hulɗar diflomasiyya tsakanin manyan jami’an ƙasashen biyu.

Za a kuma kammala taron da sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama (Memoranda of Understanding) da suka shafi kasuwanci, zuba jari, tsaro da haɗin gwiwar al’adu.

Shugaban Ƙasar zai kuma shaida sanya hannu kan yarjejeniyar kuɗi ta fam miliyan 746 tsakanin UK Export Finance da hukumomin Nijeriya.

Yarjejeniyar za ta taimaka wajen gyara tashar jiragen ruwa ta Legas (Apapa Quays) da ta Tin Can Island.

Tinubu zai kuma halarci baje-kolin Nigerian Modernism da ke nuna fasaha da al’adun Nijeriya na zamani, sannan ya shiga wani taron liyafa tare da shugabannin kasuwanci na Nijeriya da Birtaniya, da kuma ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje (diaspora).

Daga cikin tawagar shugaban ƙasar akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi; Ministan Ma’adinai, Dele Alake; da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris.

Sauran sun haɗa da Karamin Ministan Harkokin Waje, Bianca Ojukwu; Ministan Kuɗi, Wale Edun; Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwole; da Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa.

Haka kuma Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Bosun Tijani; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya); Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, da Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed, suna cikin tawagar.

Ana sa ran Shugaban Ƙasar zai dawo Nijeriya bayan kammala ziyarar ƙasar.

Tags: BirtaniyaRemiTinubuSarkiCharlesIIITinubuziyara
Previous Post

Yadda na ji da aka tuɓe ni daga sarautar Kano – Sarki Sanusi

Next Post

Maiduguri: Mutum 23 suka rasu, 146 suka jikkata, yayin da sojoji na gargaɗin akwai ‘yan harin ƙunar baƙin wake da dama a Borno

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Maiduguri: Mutum 23 suka rasu, 146 suka jikkata, yayin da sojoji na gargaɗin akwai ‘yan harin ƙunar baƙin wake da dama a Borno

Maiduguri: Mutum 23 suka rasu, 146 suka jikkata, yayin da sojoji na gargaɗin akwai 'yan harin ƙunar baƙin wake da dama a Borno

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!