Babban Hafsan Sojin Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin sojoji sama da 28,000 tare da horas da su cikin shekara guda domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.
Shaibu ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, a birnin Makurɗi.
Ya ce shirin yana daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya take ɗauka domin ƙarfafa rundunar soji wajen tunkarar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan.
A cewar sa, baya ga shirin ƙara yawan sojoji, rundunar sojin ƙasar nan tana kuma faɗaɗa dabarun yaki da rashin tsaro ta hanyar haɗa matakan soja (kinetic) da kuma matakan hulɗa da al’umma (non-kinetic) domin samun bayanan sirri da haɗin kan jama’a.

Babban hafsan ya kuma bayyana cewa rundunar ta tura sabuwar bataliya zuwa Ƙaramar Hukumar Kwande a Jihar Binuwai domin ƙarfafa ayyukan tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin.
Haka kuma ya ce rundunar na shirin ƙara amfani da jiragen helikwafta domin inganta saurin kai ɗauki a ayyukan tsaro, musamman a aikin Operation Whirl Stroke da ke yaƙi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankin.
A nasa jawabin, Gwamna Hyacinth Alia ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da rundunar sojin ƙasa kan haɗin gwiwar da suke yi wajen rage matsalolin tsaro a jihar.
Ya ce haɗin gwiwar ya taimaka wajen rage yawan ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro daga 17 zuwa uku kacal.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa rundunar soji domin tabbatar da zaman lafiya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.







