• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gyare-gyaren tattalin arziki na gwamnatin Tinubu suna samar da bayyanannen sakamako – Idris

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
March 5, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gyare-gyaren tattalin arziki na gwamnatin Tinubu suna samar da bayyanannen sakamako – Idris
Hagu zuwa dama: Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yayin ziyarar girmamawa da Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta kai wa ma’aikatar a ranar Alhamis, 5 ga Maris, 2026, a Abuja. (Hoto: Khalid Ahmed).

Hagu zuwa dama: Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yayin ziyarar girmamawa da Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta kai wa ma’aikatar a ranar Alhamis, 5 ga Maris, 2026, a Abuja. (Hoto: Khalid Ahmed).

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake aiwatarwa suna samar da sakamako a zahiri, inda ya buga misali da ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen waje da kuma cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ake sanya wa ido kan harkokin kuɗi na duniya.

Idris ya bayyana hakan ne yau Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, wadda ta kai masa ziyarar ban-girma a Abuja.

Ya ce: “A karon farko cikin shekara 13, ajiyar kuɗaɗen waje ta Nijeriya ta haura dala biliyan 50. Haka kuma, an cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da Rundunar FATF ke sanya wa ido, lamarin da ke aika saƙo mai ƙarfi ga masu zuba jari a faɗin duniya cewa Nijeriya a shirye take domin sahihin kasuwanci.”

Ministan ya jaddada cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da tallata manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya, musamman waɗanda ke da nufin inganta yanayin tattalin arziki da kuma jawo hankalin masu zuba jari.

A cewar sa, Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa ’yan Nijeriya da al’ummar duniya sun fahimci gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu take aiwatarwa da kuma damar da suke samarwa.

Ya ce: “Mu a ma’aikatar nan aikin mu shi ne mu tallafa muku, mu fito da ayyukan da kuke yi fili, tare da tabbatar da cewa mun isar da saƙon manufofi da shirye-shiryen gwamnati yadda ya kamata domin kowa ya fahimta.”

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tana ɗaukar matakai masu ƙarfi don inganta muhimman ababen more rayuwa da ke tallafa wa bunƙasar masana’antu, ciki har da gyare-gyare a ɓangaren wutar lantarki domin samar da ingantacciyar wuta ga ’yan kasuwa da masana’antu.

Ya tabbatar da cewa za su ci gaba da wayar da kai kan gyare-gyaren gwamnati tare da tallata damar zuba jari a Nijeriya a faɗin duniya.

A nata ɓangaren, Oduwole ta ce manufar ziyarar tasu ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai domin inganta yayata shirye-shirye da alƙibilar manufofin ma’aikatar ta, musamman a daidai lokacin da Nijeriya take ƙoƙarin bunƙasa masana’antu, faɗaɗa harkokin kasuwanci da kuma ƙara fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje ba tare da dogaro da man fetur ba.

Ta ce ma’aikatar ta tana mai da hankali ne wajen samar da buƙatar kayayyakin Nijeriya a matakin shiyya da na duniya baki ɗaya, ƙarfafa ƙarfin masana’antu a cikin gida, da kuma jawo muhimman zuba jari domin sauya fasalin tattalin arzikin ƙasa.

“Bayar da labarin abin da muka aikata nauyi ne da ke kan mu a matsayin gwamnati. Duba da ayyukan da aka yi cikin shekaru uku da suka wuce, yana da muhimmanci mu fito da hujjoji a sarari kan gyare-gyaren da aka aiwatar,” inji ta.

Oduwole ta yi nuni da yadda Nijeriya take taka rawa a tsarin kasuwanci na duniya da na yankuna, ciki har da Yankin Cinikayya na Nahiyar Afrika, domin bai wa ’yan kasuwar ƙasar nan damar yin gogayya yadda ya kamata a kasuwannin yankuna da na duniya.

Taron ya samu halartar manyan jami’an Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da hukumomin ta, da kuma jami’ai daga Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari.

Tags: gyare-gyareJumokeOduwoleMohammedIdrisziyaraZubaJari
Previous Post

Nijeriya za ta yi ƙarin sojoji 28,000 cikin shekara guda — COAS

Next Post

NAHCON da kamfanin Saudiyya sun ɗauki matakin daidaita tsare-tsare gabanin aikin Hajji

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
NAHCON da kamfanin Saudiyya sun ɗauki matakin daidaita tsare-tsare gabanin aikin Hajji

NAHCON da kamfanin Saudiyya sun ɗauki matakin daidaita tsare-tsare gabanin aikin Hajji

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!