Ƙaramin Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dakta Iziaq Adekunle Salako, ya ce a Nijeriya, dalilan da za a iya kauce wa kamar rashin maganin cututtukan kunne, yawan fuskantar amo mai ƙarfi, kamuwa da cututtuka a lokacin ɗaukar ciki, da ƙarancin ayyukan gwajin gano matsalar ji da wuri, suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara.
Ministan ya bayyana haka ne a yau cikin wata sanarwar manema labarai domin bikin Ranar Ji ta Duniya ta 2026, wani shiri na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wanda ke da nufin wayar da kai kan muhimmancin lafiyar ji da kuma rigakafin asarar ji.
Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya ta ce taken bikin na bana, “Daga Al’umma zuwa Ajujuwa: Kula da Lafiyar Ji Ga Kowane Yaro,” yana jaddada buƙatar haɗa kai ta hanya mai tsari wadda za ta haɗa wayar da kan al’umma da matakan da ake ɗauka a makarantu domin tabbatar da cewa babu wani yaron Nijeriya da aka bari a baya.
A cewar ta, “Ji wani ginshiƙi ne na sadarwa, koyo da kuma cuɗanya a cikin al’umma. Ga yara kuwa, yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasar tunani, nasarar karatu da walwalar zuciya.”
A faɗin duniya, fiye da yara miliyan 34 suna rayuwa da matsananciyar matsalar rashin ji, inda ƙasashe masu ƙaramin da matsakaicin kuɗaɗen shiga ke ɗauke da babban nauyin wannan matsala.
Dakta Salako ya yi nuni da cewa idan ba a magance matsalar ba, tana iya jawo jinkirin bunƙasar magana, rashin kyakkyawan sakamakon karatu, da kuma dogon lokaci na ƙalubalen tattalin arziki da zamantakewa.
“Abin lura shi ne, ana kauce wa kusan kashi 60 cikin ɗari na matsalar rashin ji a yara ta hanyar ɗaukar matakan gaggawa da suka haɗa da rigakafi, gano matsalar da wuri, da kuma kula da kunne yadda ya kamata,” inji shi.
Salako ya ba da sanarwar cewa bisa ga shawarwarin Hukumar Lafiya ta Duniya, Gwamnatin Tarayya ta faɗaɗa aikin Shirin Kula da Lafiyar Ido na Ƙasa domin ya haɗa da daidaita ayyukan da suka shafi kunne, ji da sauran lafiyar sassan azanci.
“Yanzu ana kiran shirin da suna Shirin Ayyukan Lafiyar Ido, Kunne da Sassan Azanci na Ƙasa,” inji shi, yana mai ƙarawa da cewa, “Wannan faɗaɗawa ta ƙarfafa daidaituwar ayyuka a matakin ƙasa kuma tana nuna jajircewar gwamnati wajen rage nauyin matsalar rashin ji a faɗin Nijeriya.”
Domin tabbatar da aiwatar da shirin a faɗin ƙasa, Ministan ya ce an faɗaɗa aikin Jami’an Teburin Lafiyar Ido a duk jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya domin ya haɗa da lafiyar ji, sannan ma’aikatar tana shirya tsare-tsaren shugabanci, manufofi da ƙa’idojin ƙasa domin tabbatar da cewa an shigar da lafiyar ji da sauran sassan azanci cikin tsarin kiwon lafiya.
Salako ya sake jaddada cewa ma’aikatar ta fahimci cewa ingantacciyar kula da lafiyar ji tana farawa ne daga cikin al’umma, yana mai cewa dole ne a bai wa iyaye, masu kula da yara da ma’aikatan kiwon lafiya na matakin farko ƙarfi da ilimi domin su gane alamun farko kamar jinkirin amsawa ga sauti, yawan ciwon kunne ko jinkirin magana, tare da neman kulawa cikin gaggawa.
Ya ce: “Makarantu ma suna da muhimmanci ƙwarai. Gwamnati ta himmatu wajen faɗaɗa gwajin ji ga jarirai, ƙaddamar da binciken ji na yau da kullum a makarantun firamare, horas da malamai domin gano alamun farko na matsalar ji, da kuma inganta ajujuwan da suka dace da masu matsalar ji.”
Ministan ya yi kira ga iyaye, malamai, ma’aikatan lafiya, abokan hulɗar cigaban ƙasa, ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai da su haɗa kai wajen kare lafiyar jin yara.
“Matakai masu sauƙi kamar kare yara daga amo mai ƙarfi, tabbatar da yin rigakafi a kan lokaci, da kuma ƙarfafa duba ji a kai a kai na iya hana yawancin matsalar rashin ji a yara,” inji shi.
Salako ya ce: “Gwamnatin Tarayya tana hangen tabbatuwar Nijeriya inda kowane yaro zai iya ji raɗau — daga sautukan rayayyun al’ummominsu zuwa darussan da ake koyarwa a ajujuwan su — kuma ta himmatu wajen tabbatar da kula da lafiyar ji ga kowane yaro.”







