• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotun Kano ta yanke wa wata mata hukuncin ɗaurin shekaru biyar kan zambar zuba jari

ALI KANO by ALI KANO
February 18, 2026
in Labarai
A A
0
Kotun Kano ta yanke wa wata mata hukuncin ɗaurin shekaru biyar kan zambar zuba jari

Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Kano ta samu wata mata mai suna Madam Janet Theophilus Ɗanjuma da laifin zambar zuba jari har na N22,350,000 (naira miliyan ashirin da biyu da dubu ɗari uku da hamsin) inda ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari.

Sashen Kano na Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ce ta gurfanar da wadda ake tuhumar a gaban Mai Shari’a S.M. Shu’aibu a ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, bisa tuhuma guda ɗaya da ta shafi karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.

Tuhumar ta farko ta ce: “Ke, Janet Theophilus Ɗanjuma, ma’aikaciyar Taj Bank Limited, reshen Na’ibawa, Kano, a wani lokaci cikin watan Oktoba, 2024 a Kano, cikin hurumin wannan kotu mai daraja, da niyyar damfara, kin karɓi jimillar N22,350,000 (naira miliyan ashirin da biyu da dubu ɗari uku da hamsin) daga hannun Wade Bamaiyi, da sunan cewa za a zuba kuɗin a shirin CASA na Taj Bank Limited, alhali kin san wannan magana ƙarya ce, wanda hakan ya saɓa wa Sashe na 1(1)(b) na Dokar Damfarar Kuɗi da Sauran Laifukan da ke da Alaƙa da Zamba ta 2006, kuma hukuncin sa yana ƙarƙashin Sashe na 1(3) na wannan doka.”

Bayan an karanta mata tuhumar, ta amsa laifin ta.

Bayan amsa laifin nata, lauyan masu gabatar da ƙara, Sadiq Huseini, ya gabatar da bayanan gaskiyar lamarin, inda ya bayyana yadda wadda ake tuhumar ta yaudari waɗanda abin ya shafa ta hanyar amfani da sunan wani halastaccen samfurin kuɗi domin samun amincewar su.

Ya roƙi kotu da ta same ta da laifi tare da yanke mata hukuncin da ya dace kamar yadda doka ta tanada.

A sakamakon haka, Mai Shari’a Shu’aibu ya samu Janet Theophilus Ɗanjuma da laifi tare da yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru biyar ba tare da zaɓin biyan tara ba.

Janet Ɗanjuma ta samu wannan hukuncin ne bayan ta damfari waɗanda abin ya shafa ta hanyar sanya su zuba jimillar N22,350,000 a wani shirin zuba jari na bogi, ta yi ƙaryar cewa za ta tura kuɗin cikin shirin Taj Bank CASA (Asusun Ajiya na Current Account Savings Account).

Sai dai binciken hukumar EFCC ya gano cewa an tura dukkan kuɗaɗen zuwa asusun ta na ƙashin kan ta.

Shi ne aka gurfanar da ita a gaban kotu kuma aka same ta da laifi.

Janet Theophilus Ɗanjuma, mai laifi
Tags: BankinTajdamfaraEFCCJanetTheophilusƊanjumaKanokotu
Previous Post

Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026

Next Post

Taƙaddamar Imam Ghazali Da Ibn Rushud A Kan Ruhi (Rai)

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Taƙaddamar Imam Ghazali Da Ibn Rushud A Kan Ruhi (Rai)

Taƙaddamar Imam Ghazali Da Ibn Rushud A Kan Ruhi (Rai)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!