Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya yaba da amincewar da Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta yi na ba Nijeriya kujerar dindindin a Hukumar Gudanarwar Cibiyar Kuɗi ta Afrika (AMI).
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana matuƙar farin cikin sa kan matakin da taron shugabannin ƙasashen Tarayyar Afrika (AU) karo na 39 ya ɗauka na amincewa da zama mamba ta dindindin na Nijeriya a Hukumar Gudanarwar Cibiyar Kuɗi ta Afrika (AMI).
An yanke wannan shawarar ce a taron ƙoli na watan Fabrairu 2026 da aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Amincewar ta biyo bayan sahalewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Afrika ta yi a zaman ta na 48.
Cardoso ya bayyana wannan ci gaba a matsayin nasara ga Nijeriya da kuma babban mataki ga haɗin kan Afrika da ‘yancin kuɗaɗen nahiyar.
Cibiyar AMI, wadda aka kafa a ƙarƙashin shirin cibiyoyin kuɗi na AU, ana kallon ta a matsayin mataki na share fage ga kafuwar Babban Bankin Afrika (ACB), wanda za a kafa hedikwatar sa a Abuja, Nijeriya.
Gwamnan CBN ya jaddada cewa karɓar baƙuncin AMI da kuma ACB nan gaba na da matuƙar muhimmanci ga Nijeriya da ma nahiyar baki ɗaya.
Ya ce hakan zai ƙara wa Nijeriya tasiri da murya wajen tsara tsarin kuɗi guda na bai-daya na Afrika.
Haka kuma Cardoso ya yaba wa matakin da ya ba Nijeriya damar zama mamba ta dindindin a Majalisar Daidaiton Tattalin Arziki, inda Cardoso ɗin ya ce wannan hukunci na tarihi wata muhimmiyar alama ce a tafiyar Afrika ta haɗin kan harkokin kuɗi tare bai-daya.







