• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin ‘Mission 300’ ginshiƙi ne a dabarun tsara tattalin arzikin Nijeriya – Edun

ALI KANO by ALI KANO
February 6, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Shirin ‘Mission 300’ ginshiƙi ne a dabarun tsara tattalin arzikin Nijeriya – Edun
Ministan Tattalin Arziki mai kula da daidaitawa, Mista Wale Edun, a wajen taron

Ministan Tattalin Arziki mai kula da daidaitawa, Mista Wale Edun, a wajen taron

Ministan Kuɗi kuma Ministan Daidaita Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ya bayyana cewa Mission 300, wani shiri na nahiyar Afrika da ke da nufin faɗaɗa samar da wutar lantarki da bunƙasa tattalin arziki, ginshiƙi ne a dabarun tsara tattalin arzikin Nijeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a wannan makon a Abuja lokacin da ya gana da abokan hulɗa na duniya a fannin makamashi da kuɗi kan wannan shiri.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan hanzarta aiwatar da shirin da kuma tara jarin zuba hannun jari domin ƙarfafa ɓangaren wutar lantarki na Nijeriya, tare da amincewa cewa tabbatacciyar wutar lantarki muhimmiya ce ga haɓakar aiki, faɗaɗa masana’antu, haɗa jama’a cikin tsarin dijital, da samar da ayyukan yi.

A wajen taron, Edun ya jaddada fara rungumar yarjejeniyar (Compact) da ƙasar ta yi da wuri, kafa haɗaɗɗen sashen aiwatarwa tsakanin Ma’aikatar Kuɗi da Ma’aikatar Wutar Lantarki, da kuma ƙaruwa a fannin makamashin sabuntawa da ake rabawa kai-tsaye, wanda ke samun goyon baya ta hanyar sababbin hanyoyin samar da kuɗi da haɗin gwiwa da ɓangaren ‘yan kasuwa masu zaman kan su.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki mai kula da daidaitawa, Mista Wale Edun, tare da Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, a yayin taron

Daraktar Gudanarwa ta Ayyuka a Bankin Duniya, Anna Bjerde, ta yaba da cigaban sauye-sauyen da Nijeriya ke yi, tana mai bayyana ƙasar a matsayin wacce za ta iya sauya yanayi a shirin ‘Mission 300’ sakamakon girma da jagorancin ta.

Ta ƙara da cewa shirye-shiryen da ake aiwatarwa yanzu haka suna ƙara yawan masu samun wutar lantarki.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya jaddada daidaituwar shirin da manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai ambaton cigaban da ake samu a gyaran ɓangaren wutar lantarki, saka mitoci, sake fasalin rarraba lantarki, da haɗa tsarin wutar lantarki a matakin yanki.

Dukkan ɓangarorin sun amince da hanzarta aiwatar da shirin, jawo manyan jarin kuɗi, da tabbatar da cewa ‘Mission 300’ ya haifar da tasirin tattalin arziki da ’yan Nijeriya za su iya aunawa.

Dandazon mahalarta taron
Tags: AdebayoAdelabuAnnaBjerdelantarkimakamashiMission300WaleEdun
Previous Post

Ɗan Lamiɗo a garin Lamiɗo

Next Post

Gaba dai, gaba dai CBN: Ma’aunin yawan hadahadar masana’antu, kamfanoni da kasuwanci ya kai maki 55.7 a Janairu

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Gaba dai, gaba dai CBN: Ma’aunin yawan hadahadar masana’antu, kamfanoni da kasuwanci ya kai maki 55.7 a Janairu

Gaba dai, gaba dai CBN: Ma'aunin yawan hadahadar masana'antu, kamfanoni da kasuwanci ya kai maki 55.7 a Janairu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!