Wata rundunar Sojin Nijeriya ta karkashe ’yan ta’adda da dama a wani gagarumin samame da ta kai kan sansanin shahararren shugaban ’yan bindiga, Gwaska Ɗan Karmi, da ke Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.
Rundunar ta ce harin haɗin gwiwa ne na ƙasa da sama, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soji ta 8, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce dakarun, ƙarƙashin Sashe na 2 na Operation Fansan Yamma, su ne suka gudanar da aikin.
Osoba ya ce bayanai sun nuna cewa ’yan bindiga fiye da 100 sun hallara a sansanin domin shirya manyan hare-hare kan al’ummomin da ke kusa da kuma wuraren kayan agajin soji.
Bayan sa ido na kwanaki a asirce, dakarun sojin ƙasa tare da goyon bayan Rundunar Sojin Sama (NAF) suka kai farmaki a ranar 31 ga Janairu, lamarin da ya haddasa musayar wuta.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sun yi ƙoƙarin kewaye sojojin, amma an yi amfani da ƙarfin makamai da dabarun soji aka fatattake su.
An kashe da dama daga cikin su, yayin da wasu suka tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga. Daga bisani, an ƙona sansanin kafin sojojin su janye.
Osoba ya ce Rundunar Sojin Sama na ci gaba da kai hare-haren tsare hanya domin kama ’yan bindigar da suka gudu, yayin da dakarun ƙasa ke ci gaba da mamaye yankin domin hana su sake taruwa.
Ya jaddada cewa sojoji za su ci gaba da kai hare-hare domin murƙushe ’yan bindiga a faɗin yankin Arewa-maso-yamma.







