• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Minista ya yi alhinin rasuwar babban ɗan jarida Yakubu Mohammed

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
January 14, 2026
in Labarai
A A
0
Minista ya yi alhinin rasuwar babban ɗan jarida Yakubu Mohammed
Marigayi Malam Yakubu Mohammed

Marigayi Malam Yakubu Mohammed

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga al’umma da gwamnatin Jihar Kogi bisa rasuwar babban ɗan jarida, ƙwararren ɗan siyasa, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa mujallar Newswatch, Malam Yakubu Mohammed.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, Idris ya bayyana rasuwar ɗan jaridar a matsayin babban rashi ga fannin yaɗa labarai na Nijeriya—sana’ar da ya sadaukar wa sama da shekaru hamsin na rayuwar sa.

Ya yaba wa marigayin bisa jajircewar sa wajen tabbatar da gaskiya a aikin jarida, bincike mai zurfi, da kuma ƙarfin halin gaya wa hukuma gaskiya, ko da a lokutan mulkin soja.

Ya ce: “Marigayi Yakubu Mohammed ya kasance babban jigo a fannin aikin jarida, inda ya share fagen sabon salon aiki tare da kafa harsashin bincike mai zurfi a Nijeriya, wanda ya zama ƙashin bayan sa ido kan ayyukan gwamnati da shugabanci a tsarin dimokuraɗiyyar mu.”

Ya ƙara da cewa, “Tare da abokan aikin sa da suka kafa Newswatch, gurbin da suka bari da kuma nasarorin da suka cimma na ci gaba da zama abin koyi ga matasan ’yan jarida, ba kawai wajen riƙe alƙalami ba, har ma da yin amfani da shi wajen kawo sauye-sauye a zamantakewa da siyasar al’umma.”

Haka kuma, Ministan ya bayyana Yakubu Mohammed a matsayin mai kishin ƙasa na gaske wanda ya yi imani da Nijeriya, jarumi wanda ya nuna juriya a lokacin fargaba, kuma mai kawo sauyi wanda ya yi amfani da basirar sa wajen ciyar da jama’a gaba, musamman a lokacin da yake matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU).

Idris ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin, sannan ya yi kira ga iyalai da dukkan waɗanda rashin ya shafa da su yi alfahari da kuma samun natsuwa daga kyawawan ayyukan da ya bari, waɗanda aka tattara a cikin littafin tarihin rayuwar sa mai suna “Beyond Expectations,” wanda aka ƙaddamar a watan Nuwamba 2025.

Shi dai Yakubu Mohammed ya rasu ne yana da shekaru 75, kuma ya rasu ƙasa da wata biyu bayan rasuwar ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa Newswatch, wato Mista Dan Agbese, a ranar 17 ga Nuwamba, 2025.

Tags: MohammedIdrisNewswatchrasuwata'aziyyaYakubuMohammed
Previous Post

Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ƙulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki a jami’o’i

Next Post

Za mu ba hukumar ƙidaya goyon baya, inji Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano
Siyasa

Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano

May 5, 2026
Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Next Post
Za mu ba hukumar ƙidaya goyon baya, inji Ministan Yaɗa Labarai

Za mu ba hukumar ƙidaya goyon baya, inji Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!