• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan soja domin tsaro

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
January 13, 2026
in Tsaro
A A
0
Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan soja domin tsaro
Ana sauke kayan soja da Amurka ta kawo Nijeriya daga kan jirgi

Ana sauke kayan soja da Amurka ta kawo Nijeriya daga kan jirgi

Amurka ta kawo kayan aikin soja ga hukumomin tsaron Nijeriya domin ƙarfafa ayyukan tsaro a wasu sassan ƙasar nan.

An bayyana hakan ne a wani saƙo da Rundunar Sojin Amurka a Afrika (AFRICOM) ta wallafa a shafin X a yau Talata.

“Dakarun Amurka sun miƙa muhimman kayan aikin soja ga abokan hulɗar mu na Nijeriya a Abuja. Wannan miƙawar na tallafa wa ayyukan da Nijeriya ke ci gaba da yi tare da jaddada haɗin gwiwar mu ta tsaro,” inji saƙon.

Gwamnatin Tarayya ta ce gwamnatin Amurka ta tabbatar da shirin ta na zurfafa haɗin gwiwar tsaro da Nijeriya, ciki har da samar da ingantaccen tallafin bayanan sirri, kayan tsaro da sauran kayayyaki domin ƙarfafa ayyukan da ake yi na yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a ƙasar nan.

A watan Nuwamban da ya gabata, gwamnatin ta aika wata tawaga zuwa birnin Washington da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu da kuma buɗe sababbin hanyoyin haɗin kai.

Tawagar, wadda Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro na Ƙasa (NSA), Nuhu Ribaɗu, ya jagoranta, ta gana da manyan jami’ai a Majalisar Dokokin Amurka, da Ofishin Addini na Fadar White House, da Ma’aikatar Harkokin Waje, da Majalisar Tsaron Ƙasa, da kuma Ma’aikatar Tsaro.

Membobin tawagar sun haɗa da Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi; Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Leƙen Asirin Tsaro, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun; da wakilai biyu daga Ofishin NSA.

A yayin taron, tawagar Nijeriya ta musanta zargin kisan ƙare dangi da aka ce ana yi a Nijeriya, tana jaddada cewa hare-haren tashin hankali na shafar iyalai da al’umma ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Haka kuma, ta yi watsi da yadda ake karkatar da bayanin halin da ake ciki, tana cewa irin wannan bayani zai ƙara raba ’yan Nijeriya ne kawai tare da gurɓata gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasa.

“Tattaunawar ta ba da dama mai yawa wajen gyara kuskuren fahimta game da Najeriya, ta samar da haɗin gwiwa mai ma’ana da Amurka bisa neman mafita, ta ƙarfafa amincewa tsakanin ɓangarorin biyu, tare da inganta tsari na bai ɗaya wajen kare al’umma masu rauni, musamman a yankin Midil Bel,” inji sanarwar da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar.

A cewar Onanuga, ƙasashen biyu sun amince da aiwatar da tsarin haɗin gwiwa wanda ba ya ɗaurewa doka, tare da kafa Ƙungiyar Aiki ta Haɗin Gwiwa (Joint Working Group) domin tabbatar da tsari guda da haɗin kai a fannoni da aka amince da su.

Ya ce a nasu ɓangaren, tawagar Nijeriya ta sake tabbatar da ƙudirin gwamnati na ƙarfafa matakan kare fararen hula.

“Gwamnatin Tarayya na sake jaddada sanin ta game da ƙaruwa da damuwa kan ’yancin addini da tsaro, tare da ƙarfafa ’yan ƙasa su kwantar da hankalin su cewa ana ɗaukar matakai masu ƙarfi, gaggawa, kuma masu haɗin kai domin tabbatar da tsaron ƙasa.

“Haka kuma, Amurka ta bayyana shirin ta na bayar da tallafi na ƙarin taimako, ciki har da agajin jinƙai ga al’ummomin da abin ya shafa a Midil Bel, da kuma tallafin fasaha domin ƙarfafa hanyoyin gargaɗin wuri,” inji Onanuga.

Tags: AFRICOMAmurkaBayo OnanugaSojan Nijeriya
Previous Post

Shari’ar cin hanci ta Malami ta fara ne tun kafin a naɗa ni shugaban EFCC, inji Olukoyede

Next Post

Nijeriya da Dubai za su karɓi baƙuncin taron Investopia a Legas – Tinubu 

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Nijeriya da Dubai za su karɓi baƙuncin taron Investopia a Legas – Tinubu 

Nijeriya da Dubai za su karɓi baƙuncin taron Investopia a Legas - Tinubu 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!