• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Shari’ar cin hanci ta Malami ta fara ne tun kafin a naɗa ni shugaban EFCC, inji Olukoyede

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
January 13, 2026
in Labarai
A A
0
Shari’ar cin hanci ta Malami ta fara ne tun kafin a naɗa ni shugaban EFCC, inji Olukoyede
Daga hagu: Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mista Ola Olukoyede, da tsohon Ministan Shari'a, Alhaji Abubakar Malami

Daga hagu: Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mista Ola Olukoyede, da tsohon Ministan Shari'a, Alhaji Abubakar Malami

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mista Ola Olukoyede, ya ƙaryata zargin cewa gurfanar da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, da ake yi a yanzu tana da nasaba da ƙiyayyar kai-da-kai ko dalilan siyasa.

Ya jaddada cewa shari’ar ta same shi ne tun kafin ya karɓi ragamar shugabancin hukumar.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata hira da ya yi a tashar talbijin ta Channels, inda ya yi bayani kan raɗe-raɗin da ke yawo a tsakanin jama’a game da matakin EFCC na gurfanar da tsohon ministan shari’ar bisa zargin cin hanci.

A cewar sa, binciken da ake yi kan zargin almundahanar kuɗi da ake danganta wa Malami ya fara ne tun kafin naɗin nasa, yana mai jaddada cewa doka ta wajabta wa hukumar bin duk wata shari’a mai inganci ba tare da la’akari da wanda abin ya shafa ba.

“Ba ni da wata matsala ta kai-da-kai da Malami. Na tarar da fayilolin shari’ar a nan. Shari’o’i ne da na gada,” inji shi.

Olukoyede ya ƙara da cewa EFCC hukuma ce da ke aiki bisa doka da bin ƙa’ida, babu son rai, jinƙai ko nuna wariya.

Ya ce: “EFCC hukuma ce, ba ta aiki bisa ra’ayi ko muradun kai-da-kai. Da zarar akwai fayil ɗin shari’a da hujjojin da suka isa a ci gaba, wajibi ne mu bi dukkan ƙa’idojin doka.”

Ya kuma bayyana cewa ci gaba da gudanar da aiki shi ne ginshiƙin aikin ta na yaƙi da cin hanci, yana mai cewa sauyin shugabanci ba ya soke bincike ko shari’o’in da ake gudana.

Ya ce: “Idan ka shigo irin wannan ofis, kana gadon dukiya da basussuka. Kana kuma gadon bincike. Doka ba ta ba mu damar zaɓar wanda za mu bincika ko gurfanarwa bisa dangantaka ta kai-da-kai ba.”

A Disamba 2025 ne dai EFCC ta gurfanar da Malami a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin almundahanar kuɗi da sauran laifukan kuɗi.

An gurfanar da tsohon ministan tare da ɗan sa, Abubakar Abdul’aziz Malami, da matar sa, Asabe Bashir, dangane da shari’ar.

Mutanen uku suna fuskantar tuhume-tuhume guda 16 da EFCC ta shigar, waɗanda suka shafi zargin mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba, karkatar da kuɗaɗen jama’a, da kuma wanke kuɗin da ake zargin an samo su ta hanyoyin cin hanci a lokacin da Malami ya riƙe muƙamin babban jami’in shari’ar Nijeriya tsakanin 2015 zuwa 2023.

A lokacin gurfanarwar, Malami ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa. Daga bisani, lauyoyin sa sun bayyana shari’ar a matsayin ta siyasa, tare da alƙawarin ƙalubalantar ta da ƙarfi a kotu.

Sai dai Olukoyede ya yi watsi da zargin farautar mutane da gangan, yana mai jaddada cewa matakan EFCC suna tafiya ne bisa hujjoji da bin doka kawai.

“Ba ma gurfanar da mutane saboda siyasa. Muna gurfanar da shari’o’i. Kotuna ne za su tantance ko mutum ba shi da laifi ko kuma yana da laifi,” inji shugaban na EFCC.

Ya tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa hukumar za ta ci gaba da aiki cikin gaskiya, adalci da riƙon amana, yana mai ƙara da cewa duk wanda ake zargi—ba tare da la’akari da matsayi, tasiri ko muƙamin da ya taɓa riƙewa ba—za a bi da shi daidai gwargwadon abin da doka ta tanada.

Tun daga lokacin, Babbar Kotun Tarayya ta ɗage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci na gaba domin fara shari’a, yayin da tsarin shari’a ke ci gaba.

Tags: Abubakar Malamialmundahanacin hanci da rashawaEFCCOla Olukoyede
Previous Post

Tinubu ya sauka Abu Dhabi don halartar taron ADSW 2026

Next Post

Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan soja domin tsaro

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan soja domin tsaro

Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan soja domin tsaro

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!