Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada cewa sahihan hare-haren da rundunar sojin Amurka ta kai kan manyan sansanonin ‘yan ta’addar Islamic State (ISIS) guda biyu da ke cikin dajin Bauni a yankin Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato, an aiwatar da su ne da cikakkar amincewar gwamnatin Nijeriya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayar da wannan tabbaci a cikin wata sanarwar manema labarai da ya saki a ranar Juma’a, inda ya ce: “Bayanan sirri sun tabbatar da cewa waɗannan wurare ana amfani da su ne a matsayin wuraren taruwa da shirye-shiryen kai hare-hare na ‘yan ISIS baƙin haure inda suke shigowa Nijeriya daga yankin Sahel, tare da haɗin gwiwar wasu ‘yan ta’adda na cikin gida, domin tsarawa da aiwatar da manyan hare-haren ta’addanci a cikin ƙasar nan.”
Ya ƙara da cewa an aiwatar da hare-haren ne tsakanin ƙarfe 00:12 zuwa 01:30 na safiyar Juma’a, 26 ga Disamba, 2025, “bayan samun cikakkiyar amincewa daga Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.”
A cewar Idris, “An gudanar da aikin ne bisa tsare-tsaren umurni da kulawa da aka tanada, tare da cikakken sa-hannun Rundunar Sojin Nijeriya, kuma a ƙarƙashin kulawar Ministan Tsaro da Ministan Harkokin Waje, da kuma Shugaban Rundunar Soji.
“An ƙaddamar da hare-haren ne daga dandamalin ruwa da ke Tekun Ginia, bayan an daɗe ana tattara bayanan sirri, tare da tsare-tsaren aiki da binciken wurare.
“An yi amfani da makamai masu linzami guda 16, ta hanyar jiragen sama marasa matuƙa irin MQ-9 Reaper, lamarin da ya yi nasarar tarwatsa ‘yan ISIS da aka nufa waɗanda ke ƙoƙarin kutsowa Nijeriya ta hanyar hanyar Sahel.
“A yayin aikin, wasu ɗaiɗaikun makamai da aka yi amfani da su sun faɗo a Jabo, Karamar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sakkwato, da kuma a Offa, Jihar Kwara, kusa da harabar wani otal. Ba a dai samu asarar rayukan fararen hula ba a ko’ina daga cikin wuraren, kuma hukumomin da suka dace sun gaggauta kulle wuraren.”
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake tabbatar da ƙudirin ta na fuskanta, raunana da kawar da barazanar ta’addanci, musamman waɗanda ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na ƙasashen waje ke haifarwa domin raunana ikon ƙasa da tsaron Nijeriya.
“Har ila yau, Nijeriya tana nan daram tare da abokan hulɗar ta wajen tsara dabaru da abokan Nijeriya don aiwatar da ayyuka na bai-ɗaya domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya, tsaron iyakoki da kwanciyar hankali a yankin,” inji shi.
Ya tabbatar wa da jama’ar ƙasar nan cewa gwamnati tana da cikakken iko kan tsarin tsaron ƙasa kuma ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyi.
“An shawarci ‘yan ƙasa da su zauna cikin kwanciyar hankali tare da kasancewa masu lura, yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakan gaggawa kan dukkan ƙungiyoyin ta’addanci da ke barazana ga ƙasa,” inji Ministan.






