Gwamnatin Tarayya ta kammala horar da fiye da matasa 7,000 da aka ɗauka aiki a matsayin Dogaran Daji a jihohi bakwai da ake ganin suna fuskantar matsananciyar barazanar tsaro.
Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Presidential Forest Guards Initiative da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar a watan Mayu domin dawo da ikon gwamnati a cikin dazuzzuka da ke ƙara zama mafakar ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.
An gudanar da bikin yaye ɗaliban a yau Asabar a jihohi Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Neja, Kwara da Kebbi, inda kowane ɓangare na horon ya kasance mai tsauri da tsari, domin gina dakaru masu ƙwarewa da jajircewa wajen aikin cikin daji da wuraren da ba a iya shiga cikin sauƙi.
A bayanin da ya gabatar a bikin yaye su, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaron Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana shirin a matsayin “mataki mai ƙarfi” wajen dawo da zaman lafiya da kare al’ummomi.
Ya ce: “Waɗannan Dogaran Dajin ba kawai ma’aikata ba ne da suka sa kaya. Su ne masu kare al’umma, masu tarin bayanai, kuma ginshiƙi a cikin tsarin tsaron mu.
“Za su tsaya a ƙasa, su wanke wuraren da masu aikata laifi ke ɓuya, su kuma taimaka wa jami’an tsaro wajen ƙwato yankunan da miyagu suka mamaye.”
Ribaɗu ya ƙara da cewa babu wata tazara tsakanin kammala horon da fara aiki.
“Nan da nan za a tura su bakin aiki, albashin su da haƙƙoƙin su za su fara nan take,” inji shi.

An shafe watanni uku ana horar da waɗanda aka ɗauka, inda aka mayar da hankali kan:
- Horon jiki da ƙwaƙwalwa (physical & mental endurance).
- Tsallake cikas, da hanyoyin jure doguwar tafiya cikin daji.
- Horar da su kan dabarun yaƙi da tsari na tsaro (tactical drills).
- Horo kan mayar da martani yayin farmaki, da kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.
- Horon kyakkyawar mu’amala da fararen hula, kare haƙƙin bil’adama, da bin doka.
Daga cikin waɗanda suka halarci horon, kashi 98.2 cikin ɗari ne suka kammala.
An kori mutane 81 sakamakon ƙin bin ƙa’ida, yayin da biyu suka rasu saboda matsalolin rashin lafiya.
Mafi yawan su ’yan asalin yankunan da za su yi aiki ne, abin da gwamnati ta ce zai taimaka masu wajen sanin daji, hanyoyin shiga da fita, tare da samun goyon bayan al’umma.
Dogaran Dajin suna ƙarƙashin kulawar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaron Ƙasa tare da Ma’aikatar Muhalli, ƙarƙashin daidaitawar DSS da Hukumar National Park Service.
Haka kuma rundunar soji, rundunar sojin ruwan Nijeriya, rundunar ’yan sanda da NSCDC duk sun bayar da gudunmawa wajen tsari da dabarun aiki.
Gwamnoni da mataimakan su a jihohin da abin ya shafa sun halarci taron, ciki har da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da na Yobe, Mai Mala Buni, yayin da wasu jihohin suka samu wakilcin mataimakan gwamnoni.
A ƙarshe Ribaɗu ya sake jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da faɗaɗa shirin zuwa sauran jihohi, ya ce: “Idan muka kare dazukan mu, mun kare ƙasa. Idan muka kare ƙasa, mun kare rayukan al’ummar mu. Gwamnatin Tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba.”







