’Yan matan da aka sace daga Government Girls Comprehensive Senior Secondary School (GGCSS) ta Maga, a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi, sun sami ’yancin su ta hanyar amfani da dabarar tattaunawa cikin lumana (non-kinetic) da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka.
Rahotanni sun ce sakin dukkan yaran da aka sace ya samu ne ta hanyar haɗin gwiwar jami’an Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Amfani da dabarar tattaunawa cikin lumana — inda ke yin amfani da tattaunawa, sulhu da gina amana maimakon amfani da ƙarfin soja — ya nuna sauyin tsarin gwamnati wajen magance matsalolin garkuwa da mutane ta hanyar lumana.
Sace ɗaliban, wanda ya biyo bayan makamantan lamarin da suka faru a yankin, ya haifar da fargaba a faɗin ƙasa tare da sa Shugaban Hafsan Sojoji ya ba da umarnin gaggawa ga sojoji su ƙara zurfafa bincike da ceto.
Sakin ɗaliban ya zama babban abin farin ciki ga iyalan su da al’umma baki ɗaya.







