Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa gwamnatin Amurka ta tabbatar da shirin ta na zurfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ta da Nijeriya, ciki har da samar da ƙarin tallafin bayanan sirri, kayan aiki da makamantan su don ƙarfafa ayyukan yaƙi da ta’addancin da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suke yi a ƙasar.
Wannan yana zuwa ne bayan tattaunawa da muhawara da aka gudanar a makon da ya gabata tsakanin wani muhimmin kwamiti na jami’an gwamnatin Nijeriya da na Amurka, domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu tare da buɗe sababbin hanyoyin yin aiki tare.
Kwamitin, a ƙarƙashin jagorancin Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro na Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, ya gana da manyan jami’ai a Majalisar Dokoki ta Amurka, Ofishin Ɓangaren Addini na fadar White House, Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje, Kwamitin Tsaro na Ƙasa, da Ma’aikatar Yaƙi.
Membobin tawagar sun haɗa da Babban Lauyan Ƙasa, Lateef Fagbemi; Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Sashen Leƙen Asirin Tsaro, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun; da wakilai biyu daga Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa.
A cewar wata sanarwa da Mai Ba Shugaba Tinubu Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsara Dabaru, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, tawagar Nijeriya ta ƙaryata zargin kisan ƙare-dangi da aka ce ana yi a Nijeriya yayin tattaunawar da aka yi a birnin Washington, DC, inda ta jaddada cewa hare-haren tashin hankali suna shafar iyalai da al’ummomi ne a kowane addini da ƙabila.
Tawagar ta kuma yi watsi da yadda wasu ke ƙoƙarin bai wa lamarin fassara ta ƙarya, tana mai cewa irin wannan yaudarar za ta raba kan ‘yan Nijeriya kuma ta gurɓata ainihin gaskiyar abin da ke faruwa.
Ya ce: “Tattaunawar ta ba da dama sosai wajen gyara babban kuskuren da ake yi wa Nijeriya, ta kafa haɗin gwiwa mai inganci da Amurka bisa mafita, ta ƙarfafa amincewar juna, tare da haɓaka dabarun aiki tare domin kare al’ummomin da ke cikin rauni, musamman a yankin Middle Belt.
“Haka kuma Amurka ta nuna niyyar ta ta bayar da ƙarin tallafi, ciki har da agajin jinƙai ga al’ummomin da abin ya shafa a Middle Belt da tallafin fasaha don ƙarfafa hanyoyin gargaɗin fari-tashi.”
A cewar sa, ƙasashen biyu sun amince da aiwatar da wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa wadda ba ta tilastawa ba, tare da kafa Kwamitin Aiki na Haɗaka don tabbatar da tsari guda ɗaya wajen aiwatar da yarjejeniyar.
Ya ce a nata ɓangaren, tawagar Nijeriya ta sake tabbatar da jajircewar gwamnati wajen ƙarfafa matakan kare fararen hula.
“Gwamnatin Tarayya na sake jaddada san inta game da ƙara tsanani a batun ‘yancin addini da tsaro, kuma tana kira ga ‘yan ƙasa da su kwantar da hankalin su domin gwamnati tana ɗaukar matakai ƙwarara, cikin gaggawa da daidaito, saboda tabbatar da tsaron ƙasa,” inji Onanuga.
Wannan sanarwar ta Fadar Shugaban Ƙasar ta zo ne makonni bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar aikowa da sojojin Amurka zuwa Nijeriya da “bindigogi suna tashi” idan Nijeriya ba ta dakatar da abin da ya kira kisan gilla kan Kiristoci da ‘yan ta’adda ke yi ba.
Haka kuma ya ayyana Nijeriya a matsayin “Kasa Mai Babbar Matsala” kan kisan Kiristoci, yana kiran lamarin “mummunan kisan gilla.”
Trump ya ce: “Idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari a riƙa kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi da taimakon ta ga Nijeriya, kuma mai yiwuwa ta shiga wannan ƙasa da ta ɓata sunan ta yanzu, ‘ta shiga da hargitsi,’ domin kawar da ‘yan ta’addan Musulmi da ke aikata waɗannan mummunan laifuffuka,” inji shi a shafin sa na Truth Social.
“Ni yanzu ina umurtar Ma’aikatar Yaƙi da ta fara shirin yiwuwar ɗaukar mataki. Idan muka kai hari, zai kasance cikin sauri, tsanani, kuma mai daɗi,” inji Trump.
Amma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaryata zargin kisan ƙare-dangi da aka ce ana yi wa Kiristoci, yana mai tabbatar da cewa Nijeriya tana nan daram wajen mutunta ‘yancin addini da zaman lumana.







