Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance, jam’iyyar gamayyar da ake sa ran zai yi aiki da ita a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a yau Litinin ta shafin sa na X, inda ya wallafa hoton sa yana riƙe da katin zama ɗan ADC tare da gajeren rubutu: “It’s official.”
It’s official. -AA pic.twitter.com/OBoC6XdmtR
— Atiku Abubakar (@atiku) 24 ga Nuwamba, 2025
Wannan matakin nasa ya biyo bayan murabus ɗin sa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a watan Yuli, jam’iyyar da ta daɗe tana fama da rikicin cikin gida.
Atiku ya bar PDP ne makonni biyu bayan wasu ‘yan adawa sun amince suka kuma gabatar da ADC a matsayin sabon dandamalin siyasar su domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Dalilin Atiku na barin PDP
A sa’o’i bayan mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya bada sanarwar murabus ɗin sa daga PDP, Atiku ya bayyana dalilin ɗaukar wannan mataki a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 16 ga Yuli.
A cikin wasiƙar da aka aika wa shugaban PDP na Mazaɓar Jada I a Jihar Adamawa, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce akwai saɓani marasa sulhu da kuma karkacewar jam’iyyar daga manufofin da aka kafa ta a kai.

“Na rubuto wannan wasiƙa ne domin na yi murabus daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ba tare da ɓata lokaci ba” inji shi.
Atiku ya yi wa jam’iyyar da shugabannin ta fatan alheri a ayyukan su na gaba, tare da gode musu bisa goyon baya da damar da suka ba shi a tsawon shekaru.
Ya ce: “Ina yi wa jam’iyyar da shugabannin ta fatan alheri.”







