• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Hukuncin da aka yanke wa Nnamdi Kanu ya ƙara dagula matsalolin Nijeriya, inji Peter Obi

ALI KANO by ALI KANO
November 22, 2025
in Siyasa
A A
0
Hukuncin da aka yanke wa Nnamdi Kanu ya ƙara dagula matsalolin Nijeriya, inji Peter Obi
Mista Peter Obi

Mista Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ya ce hukuncin da aka yanke wa jagoran ƙungiyar ƙafa ƙasar Biyafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, ya ƙara dagula matsalolin Nijeriya maimakon rage su.

An dai yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai a ranar Alhamis a Kotun Tarayya da ke Abuja kan laifin cin amanar ƙasa.

A wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya mai taken, “Hukuncin Kanu: A Wani Lokaci Irin Wannan,” Obi ya ce: “Labarin hukuncin da aka yanke wa Mazi Nnamdi Kanu ya kamata ya sa kowane ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa ya tsaya ya yi tunani sosai. Wannan lamari ya faru ne a wani lokaci da ƙasar mu take fama da tsananin matsin tattalin arziki, rashin tsaro da illolin rashin kyakkyawan shugabanci.

‘‘Maimakon rage tayar da hankali, wannan abin takaici na iya ƙara haddasa shi.”

Ya ce tun da farko ya kasance yana jaddada cewa bai kamata a kama Kanu ba, yana mai cewa kamawa, tsarewa, sannan yanzu hukunta shi “na nuna gazawar shugabanci da rashin fahimtar matsalolin da ke tattare da lamarin.”

Ya ƙara da cewa: “Na daɗe ina nanata cewa tattaunawa, sulhu mai ma’ana, da shugabanci na kowa ne hanyar samun zaman lafiya mai ɗorewa. Tilastawa ko amfani da ƙarfi ba su zama dole sai bayan an gaza amfani da hikima. A wannan lamari, ina ganin ba wai kawai ba a gaji da amfani da hikima ba, har ma ba a binciko ta yadda ya kamata ko ma ba a bincika ta sosai ba.

‘‘Ƙorafe-ƙorafen da Kanu ya yi ba sabbi ba ne. Matsalolin da yake neman a warware ba masu wuyar warwarewa ba ne. Abin da ake buƙata shi ne hikima, tausayi, da iya sauraron jama’a. A kowace ƙasa mai aiki yadda ya kamata, ana fuskantar irin waɗannan koke-koke da tattaunawa da gyare-gyaren da ke ƙara haɗe ƙasa.”

Obi ya ce matsayar da gwamnati ta hau Kai ta ƙara lalata rashin amincewa da juna, ta kuma haifar da wata matsala da za a iya guje mata, a wani lokaci da ‘yan ƙasa ke fama da tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro.

“Yayin da wasu ke cewa ‘dole doka ta yi aikin ta,’ shugabanci a wasu lokuta yana buƙatar fiye da bin doka kai-tsaye. Ƙasashe da dama a duniya kan ɗauki matakan siyasa, sulhu ta hanyar tattaunawa, ko ma yin afuwa, idan tsarin shari’a kaɗai ba zai iya samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. Nijeriya ba daban ba ce.”

Obi ya ce yadda aka gudanar da batun Kanu ya sanya gwamnati cikin yanayi kamar mutumin da ya faɗa rami, maimakon ya nemo hanyar fita, sai ya ci gaba da tona shi. Wannan, a cewar sa, ya ƙara tsananta matsalar gwamnati da ta ƙasa baki ɗaya.

“Idan har muna son sabuwar Nijeriya – mai haɗin kai, ta zauna lafiya, kuma mai cigaba – dole shugabannin mu su zaɓi warkarwa maimakon tashin hankali, sulhu maimakon ɗaukar fansa, da tattaunawa maimakon rarrabuwar kai.

“Sai da adalci, gaskiya, da tausayi za mu iya gina makoma inda kowane ɗan Nijeriya zai ji an saurare shi, an daraja shi, kuma yana cikin amincewa.”

A ƙarshe, ya ce: “Babban kira na a wannan lokaci, ba tare da la’akari da yadda kowa ke ji game da hukuncin kotu ba, shi ne mu kasance masu fata ga zaman lafiya da sulhu, wanda a ƙarshe za a samu.

“Ina kuma kira ga Fadar Shugaban Ƙasa, Majalisar Ƙoli ta Ƙasa, da dattawan ƙasa masu kishin haɗin kai da zaman lafiya, da su tashi tsaye domin samo mafita ta dindindin.”

Tags: Biyafracin amanar ƙasaIPOBNnamdi KanuPeter Obishari'a
Previous Post

Cewar Ministan Yaɗa Labarai: Tawagar da Gwamnatin Tarayya ta tura zuwa Amurka tana samun nasarar magance labaran ƙarya game da yanayin tsaron Nijeriya

Next Post

Matsalar tsaron Nijeriya tana hana ni barci, inji Tinubu a taron cikar ACF shekaru 25

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci
Siyasa

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

April 28, 2026
A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027
Siyasa

A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

April 25, 2026
Next Post
Matsalar tsaron Nijeriya tana hana ni barci, inji Tinubu a taron cikar ACF shekaru 25

Matsalar tsaron Nijeriya tana hana ni barci, inji Tinubu a taron cikar ACF shekaru 25

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!