• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnan CBN ya yaba kan jinjina da kyakkyawar shaidar da cibiyar S&P Global ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
November 16, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Babban Bankin Nijeriya tare da Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso (Hoton CBN daga shafin: Beautiful Nigeria)

Babban Bankin Nijeriya tare da Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso (Hoton CBN daga shafin: Beautiful Nigeria)

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya nuna yabawa dangane da kyakkyawar shaida da jinjina tare da ɗaga matsayi da Cibiyar Bin-diddigin Tattalin Arziki ta Duniya, S&P Global Ratings ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya.

S&P Global Ratings dai a wani rahoton ta na baya-bayan nan, ta nuna gamsuwa da irin tsare-tsaren tsaftace hada-hadar kuɗaɗe da CBN ke yi, wanda cibiyar ta ce akwai yaƙini nan da ‘yan shekaru kaɗan masu zuwa tattalin arzikin Nijeriya zai cimma nagarta da inganci mai ɗorewa.

Rahoton na S&P Global Ratings ya ce: “A yanzu Babban Bankin Nijeriya na da kyakkyawar damar cimma muradin sa na ƙarfara tattalin arzikin Nijeriya nan da ‘yan shekaru kaɗan.”

Cardoso ya ce tun daga farkon wannan shekara ta 2025, aka fara ganin haske mai nuni da cewa tsarin hada-hada domin saisaita bunƙasa tattalin arziki yana tafiya a kan hanya ɗoɗar.

Ya ce wannan kyakkyawar shaida da aka yi wa Nijeriya na ƙara nuni da cewa yanzu a duniya an gamsu cewa Nijeriya da gaske take yi, kuma an daina shakku ko tababar makomar tattalin arzikin ƙasar nan.

Wannan rahoto da S&P ta fitar, zai ƙara zaburar da ɗimbin masu sha’awar zuba jari kwararowa da jarin su a Nijeriya, cike fa yaƙinin cewa tattalin arzikin ƙasa ba shi da wata tangarɗa.

Idan ba a manta ba, a ƙarshen watan Oktoba ma CBN ya yi farin cikin cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su, sakamakon kashin-kajin da masu aikata ta’addanci da masu zambar kuɗaɗe suka shafa wa ƙasar.

Wannan jarida ta buga labarin, inda a lokacin CBN ya bayyana cewa cire sunan Nijeriya daga ƙasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su a duniya cewa, hakan tabbaci ne da ke nuna duniya ta gamsu da tsare-tsaren tattalin arzikin da wannan gwamnati ta bijiro da su.

Cikin wata sanarwar da Daraktar Riƙon Sashen Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai, Hakama Sidi Ali, ta sa wa hannu kuma ta fitar a ranar Asabar, ta nuna cewa duniya ta gamsu da tsare-tsaren harkokin kuɗaɗe da kuma gagarumin yaƙi da almundahana da zambar kuɗaɗen da ake kan yi a Nijeriya.

CBN ya ci gaba da cewa an cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke sa-ido kan su, bayan kwamitin sa-ido ɗin ya gani tare da tabbatarwa irin “gagarumin cigaban” da Nijeriya ta samu wajen yi wa tsare-tsaren kuɗaɗe ragama da linzamin daƙile zambar kuɗaɗe da kuma datse hanyoyin safarar kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.

FATF dai ƙaƙƙarfar hukumar sa-ido ce ta duniya wadda ke lura kan hada-hada da harƙallar kuɗaɗe ta ɓarauniyar hanya. Ta bayyana cire sunan Nijeriya a ranar Juma’a, tare da ƙasashen Afrika ta Kudu, Mozambique, Burkina Faso.

Hakama Ali ta ci gaba da cewa cire sunan Nijeriya ya nuna irin kyakkyawan tasirin da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da CBN, Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Lura da Hada-hadar Kuɗaɗe ta Nijeriya (NFIU) da kuma EFCC suka yi.

Ta ce: “Rawar da CBN ya taka wajen samun wannan nasara ta shafi tabbatar da sa-ido sosai, tsara ƙa’idoji, gindaya sharuɗɗa da gudanar da ayyuka ƙeƙe-da-ƙeƙe wajen hada-hadar kuɗaɗe.”

Daga cikin tsare-tsaren da FATF tare da Kafofin Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe na Afrika ta Yamma su ka yi wa bin diddigi, akwai tsarin lambobin sirrin bibiyar Tsarin Musayar Kuɗaɗe, wadda aka ƙirƙiro domin rage harƙalla a hada-hadar musayar kuɗaɗe.

Cire Nijeriya daga ƙasashen da ake kaffa-kaffa da su ɗin zai ƙara cire shakku kan Nijeriya, tare da faɗaɗa hada-hadar cinikayya tsakanin ƙasar da ƙasashen waje, cibiyoyi da masu zuba jari. Haka bankuna za su samu ƙarin hulɗoɗi da masu son haɗin gwiwa daga waje.

An dai saka sunan Nijeriya cikin ƙasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffa da su a cikin 2021, bayan duniya ta nuna rashin amincewa dangane da yadda salon yaƙi da zambar kuɗaɗe ke gudana, musamman wajen matsalar yadda ake samun safarar muggan kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.

Tags: CBNHakama Sidi AliOlayemi Cardoso
Previous Post

Tinubu ya sabunta naɗin Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA na tsawon shekaru 5

Next Post

Daga yanzu mu ne za mu ba sojoji umarni – Matawalle

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Daga yanzu mu ne za mu ba sojoji umarni – Matawalle

Daga yanzu mu ne za mu ba sojoji umarni - Matawalle

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!