Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, shi ne ya bayyana cewa daga yanzu su ministocin tsaro su ne za su riƙa ba sojoji umurnin su yaƙi ‘yan bindiga kai-tsaye ba sai sun jira oda “daga sama” ba.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a Gusau a ranar Juma’a kan ƙarin sojoji zuwa Jihar Zamfara da Gwamnatin Tarayya ta yi domin ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga da sauran masu laifi a jihar.
“Ina nan tafe don haɗuwa da sojoji domin ba su umurnin da zai tabbatar da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da masu aikata laifuffuka a jihar,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan.
“Daga yanzu, babu wanda zai ce yana jiran umarni daga sama. Mu ne za mu bada umarni kuma za mu tabbatar an kawo ƙarshen duk wani nau’in laifi a faɗin ƙasar nan.”
Matawalle ya yaba wa magoya bayan APC bisa goyon bayan su ga Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC guda ɗaya a zaɓen 2027.
Ya kuma bayyana Tinubu a matsayin “shugaba mai hangen nesa da manufofi da shirye-shiryen da suka mayar da hankali kan al’umma.”
Ya kawo misalin gina babbar hanya mai layi biyu tsakanin Zariya zuwa Sakkwato a matsayin shaida.
Ministan ya yi kira ga ‘yan APC da su ci gaba da wayar da kan jama’a domin samun ƙarin goyon baya ga Tinubu a gabanin zaɓen gaba.







