• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, May 13, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya sabunta naɗin Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA na tsawon shekaru 5

Wakilin Mu by Wakilin Mu
November 14, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu ya sabunta naɗin Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA na tsawon shekaru 5
Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (ritaya)

Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (ritaya)

Shugaba Bola Tinubu ya sabunta nadin Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) na tsawon wa’adin shekaru biyar.

Labarin yana ƙunshe cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a yau Juma’a.

Shi dai Marwa, gwamnatin Buhari ce ta fara naɗa shi muƙamin a cikin 2021 bayan ya yi aiki a matsayin Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Kawar da Shan Miyagun Ƙwayoyi tsakanin 2018 da 2020.

Sabon naɗin zai kai tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar har zuwa shekarar 2031.

Marwa, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihohin Legas da Borno, ya samu horon soja a Nigerian Military School (NMS) da Nigerian Defence Academy (NDA).

Ya riƙe muƙamai da dama cikin rundunar sojin Nijeriya, ciki har da Brigade Major na 23 Armoured Brigade da Aide-de-Camp (ADC) ga tsohon Babban Hafsan Soji, Lt.-Gen. Theophilus Danjuma.

Ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin mai bada shawara kan Tsaro a Jakadancin Nijeriya da ke Washington DC, da mai bada shawara kan tsaro ga Wakilan Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Marwa yana da digiri na biyu a fannin Public and International Affairs daga Jami’ar Pittsburgh (1983–85) da Master of Public Administration daga Jami’ar Harvard (1985–86).

A wa’adin sa na farko, NDLEA ta samu manyan nasarori, ciki har da kama masu safarar miyagun ƙwayoyi sama da 73,000 da kuma ƙwace ƙwayoyi masu nauyin fiye da kilo miliyan 15.

Haka kuma hukumar ta gudanar da manyan shirye-shirye kan wayar da kan jama’a game da illolin shan ƙwayoyi a faɗin ƙasar nan.

Tinubu, a saƙon sa, ya bayyana sake naɗin a matsayin tabbacin gamsuwa da jajircewar Marwa wajen yaƙi da fataucin da amfani da miyagun ƙwayoyi.

Ya ce: “Ina kira gare ka da ka ci gaba da jajircewa wajen fatattakar masu safarar ƙwayoyi da ke barazana ga makomar al’ummar mu, musamman matasa.”

Tags: Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (ritaya)muggan ƙwayoyinaɗiNDLEAShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Gwamnati ta dakatar da ƙudirin ƙarin harajin kashi 15 cikin ɗari kan shigo da fetur da dizal

Next Post

Gwamnan CBN ya yaba kan jinjina da kyakkyawar shaidar da cibiyar S&P Global ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya

Related Posts

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Tsaro

Dakaru sun aika da ’yan ta’adda masu yawa barzahu, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro

May 9, 2026
Next Post
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

Gwamnan CBN ya yaba kan jinjina da kyakkyawar shaidar da cibiyar S&P Global ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!