Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya yi watsi da rahotannin da ke cewa wai ya ce zai bar wa wani mutum daban damar yin takardar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ya ce masu wannan tunanin ba su fahimci hirar sa da BBC Hausa ba ne.
A takardar sanarwa da manema labarai wadda mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Mista Paul Ibe ya fitar a yau Alhamis, Atiku ya ce an yaudari mutane da rahotannin domin kuwa a hirar babu inda ya ko alamta cewa zai bar wa wani ɗan takarar damar sa.
A cewar Ibe, da aka duba hirar da kyau, ta Hausar da ya yi da kuma fassarar ta da Turanci, an tabbatar da cewa lallai an yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar gurguwar fassara.
Ya ce: “Babu inda Wazirin Adamawa ya faɗa a bayyane ko a alamce cewa yana da niyyar sauka daga takara ya bar wa wani.
“Abin da Atiku Abubakar ya faɗa ƙarara shi ne matasa, da ma sauran ‘yan takara, suna da ‘yancin su fito su ma su yi takarar.
“Haka kuma ya nanata cewa idan aka fitar da matashin ɗan takara a zaɓen fidda gwani babu ƙumbiya-ƙumbiya, to a shirye yake ya mara masa baya ba tare da ɓata lokaci ba.”
Ibe ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da yin aiki da bada wata fassara ta daban ga abin da mutum ya faɗa, ya ce yin hakan ya saɓa wa aikin jarida kums yana haifar da rashin yarda daga jama’a.
A hirar sa da BBC Hausa, Atiku ya ce jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), wadda ya shiga kwanan baya, tana bada muhimmanci ga matasa da mata.
Ya ƙara da cewa duk da yake bai yanke shawarar ya yi takara ko a’a ba, a shirye yake ya goyi bayan duk wani matashi wanda jam’iyyar ta tsayar ta hanyar bin dukkan ƙa’idojin zaɓen share fage.
Ya ce idan ya yi takarar amma wani matashi ya yi nasara a kan sa, to zai karɓi ƙaddara domin jam’iyyar su mai ba matasa da mata muhimmanci ce.







