• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

2027: Matan Arewa sun jaddada muhimmancin sake zaɓen Tinubu

WAKILIN MU by WAKILIN MU
November 1, 2026
in Siyasa
A A
0
2027: Matan Arewa sun jaddada muhimmancin sake zaɓen Tinubu
Dandazon mahalarta taron ƙungiyar "Matan Arewa 4 Tinubu Again" (MATA) a Kano

Dandazon mahalarta taron ƙungiyar "Matan Arewa 4 Tinubu Again" (MATA) a Kano

Ƙungiyar Matan Arewa 4 Tinubu Again (MATA) ta bayyana aniyar ƙara wayar da kan mata da tattara goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Dubban mata daga sassa daban-daban ne suka hallara a Kano domin ƙaddamar da ƙungiyar, wadda ta bayyana aniyar ta ta tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake zaɓen sa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Bikin ƙaddamarwar, wanda ya haɗa da bikin bayar da lambobin yabo ga wasu masu ruwa da tsaki a harkokin yaɗa labarai, ya samu halartar mata masu goyon bayan gwamnatin Tinubu, da shugabannin siyasa da sauran manyan baƙi.

Ƙaddamar da ƙungiyar na zuwa ne a wani mataki na shirya mata a Arewa domin ƙara shiga harkokin siyasa, wayar da kan al’umma da kuma ƙarfafa goyon baya ga takarar Tinubu a zaɓen da ke tafe.

A wajen taron, Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Rediyo da Watsa Labarai, Hajiya Rahma Abdulmajid, wadda ita ce Shugabar ƙungiyar ta MATA, ta yi kira ga al’ummar Arewa da su goyi bayan kammala wa’adin mulkin shekaru takwas da Kudu ke yi, tana mai cewa mutunta tsarin karɓa-karɓar mulki zai taimaka wajen kiyaye zaman lafiyar Nijeriya da haɗin kan ƙasa.

Rahma ta bayyana cewa tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu ya taimaka wajen tabbatar da daidaito a siyasar ƙasar nan, don haka bai kamata a yi watsi da shi saboda muradin wani ɗan siyasa ba.

Ta ce Arewa ta riga ta amfana da wa’adin shekaru takwas na tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, daga 2015 zuwa 2023, saboda haka ya dace a mutunta damar da Kudu ke da ita a yanzu ƙarƙashin Tinubu.

Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Rediyo da Watsa Labarai, kuma jagorar ƙungiyar “Matan Arewa 4 Tinubu Again” (MATA), Hajiya Rahama Abdulmajid, tana gabatar da jawabi a taron

Ta ƙarfafi mata da sauran masu ruwa da tsaki da su taka rawar gani wajen wayar da kan jama’a game da muhimmancin zaman lafiya, haɗin kai da cigaban ƙasa.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Darakta-Janar na Yaɗa Labaran sa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wakilta, ya jaddada cewa adalci da bai wa kowane yanki dama su ne ginshiƙan haɗin kan Nijeriya.

Shi ma tsohon Gwamnan Jigawa kuma tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyukan raya ƙasa da dama a Arewa, musamman a fannonin sufuri da kiwon lafiya.

Ya ambaci wasu sassan babbar hanyar Abuja-Kaduna-Kano, hanyar Kaduna-Pambeguwa, hanyoyi a Jihar Kano da gadar Jimeta a Yola, tare da wasu cibiyoyin lafiya da ayyukan inganta asibitoci a jihohin Arewa.

Ƙaddamar da MATA na ƙara fito da rawar da mata za su iya takawa wajen shiga harkokin siyasa da shirya al’umma, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Tare da haɗin kan mambobin ta da sauran masu goyon baya, ƙungiyar ta bayyana kan ta a matsayin wani dandali na mata a Arewa da ke son ganin Shugaba Tinubu ya samu wa’adi na biyu.

Tags: ArewamataRahama Abdulmajidzaben2027
Previous Post

Sabon Ɗanmasanin Sakkwato, Farfesa Mansur, ya naɗa sarautun musamman

Next Post

Naɗin Sarautar Ɗanmasani A Ƙasar Hausa Da Ayyukan Sa

Related Posts

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba
Siyasa

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba

November 28, 2026
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Next Post

Naɗin Sarautar Ɗanmasani A Ƙasar Hausa Da Ayyukan Sa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!