• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
November 1, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tabbatar da naɗa kamfanoni takwas da za su riƙa gudanar da bincike da sa-ido kan jigilar ɗanyen mai da iskar gas zuwa ƙasashen waje.

Haka kuma waɗannan kamfanoni za su riƙa raba aikin lura da tashoshin lodin mai da gas a tsakanin su.

Waɗannan naɗe-naɗe sun fara aiki ne daga ranar 2 ga Oktoba, 2026, ƙarƙashin tsarin Kula da Harkokin Fitar da Kayayyaki na Nijeriya (Nigerian Export Supervision Scheme).

An bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da CBN ya fitar ranar 29 ga Oktoba, 2026, mai lamba TED/FEM/FPC/PUB/001/005, wadda Daraktar Sashen Kasuwanci da Canjin Kuɗaɗe, Aderinola Shonekan, ta sanya wa hannu.

Sanarwar, wadda aka fitar bisa tanadin dokar binciken kayayyakin da ake shirin shigo da su ƙasar nan kafin jigila ta shekarar 1996, ta shafi bankunan da aka amince da su gudanar da hada-hadar kuɗaɗen waje, Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Sama (NUPRC), Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiya da Ƙasa, masu gudanar da tashoshin lodin mai da gas, kamfanonin mai da gas da kuma sauran jama’a.

Sanarwar har ila yau a cewar CBN, ta umurci dukkan waɗannan hukumomi da kamfanoni da su tabbatar da bin sabon tsarin ka’in da na’in.

Yadda CBN Ya Raba Rashoshin Lodin Mai da Gas:

A ƙarƙashin sabon tsarin, an raba tashoshin lodin mai da gas ga kamfanonin takwas kamar haka:

Dakee Engineering and Construction Ltd: LNG, Escravos (Gas), Bonny River Terminal (BRT) da EGTL.

Sai kuma Trexem Energy Services Ltd: Egina, Qua Iboe da Tulja.

Akwai kuma Geoscape Ltd: Escravos, ERHA, Odudu da FSO Cawthorn, sai kuma 617 Ltd: Bonga, Brass, Usan da Eagle.

Akwai kuma Robinson International Energy Ltd: Ugo-Cha, Penington, Aje, Ima, Oyo da Nembe.

Kamfanin Trobell International Nigeria Ltd: Forcados, Bonny da Okwori.

Shi kuma Integrated Shipping Services Nigeria Ltd: Akpo, Antan, Okoro, Anyala-Madu da Ebok.

Kamfanin Kephren Business: Ukpokiti, Utapate, Yoho, Abo, Agbami, Ajapa, Okono, Okwok da sauran ƙananan wuraren haƙar mai da NUPRC za ta ware.

Kamfanonin da Za Su Sa Ido Kan Masu Binciken Laya:

Haka kuma, CBN ya naɗa kamfanoni biyu da za su sa-ido kan ayyukan waɗannan jami’an binciken kaya.

Kamfanin Q&Q Control Services Ltd zai sa-ido kan ayyukan 617 Ltd, Trexem Energy Services Ltd, Geoscape Ltd da Kephren Business Ltd.

A nasa ɓangaren, Arlington Securitas Nigeria Ltd zai kula da ayyukan Dakee Engineering and Construction Ltd, Trobell International Nigeria Ltd, Robinson International Energy Ltd da Integrated Shipping Services Nigeria Ltd.

Sauye-sauyen da aka yi a baya na wannan sabon mataki ya biyo bayan sauye-sauye da dama da aka yi wa tsarin kula da fitar da man fetur da iskar gas zuwa ƙasashen waje.

A watan Mayun 2024, CBN ya naɗa jami’ai 11, waɗanda suka haɗa da kamfanoni tara masu binciken kayayyakin da ake fitarwa kafin jigila da wasu kamfanoni biyu masu sa-ido da tantance ayyuka.

A lokacin, kamfanonin Dakee Engineering and Construction da Arlington Securitas na cikin waɗanda aka naɗa.

A watan Maris na 2025 kuma, bankin ya sake duba yadda aka raba tashoshin lodin mai da gas ga kamfanonin.

Haka kuma, a watan Yulin 2026, CBN ya naɗa kamfanin Candid Oil Services Ltd a matsayin jami’in bincike kan kayayyakin da ake fitarwa daga tashar ajiyar mai ta Taurus Oil and Gas Depot.

Sabuwar sanarwar ta sauya kamfanonin da ke da alhakin binciken kayayyakin da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje, tare da sake fasalin tashoshin da kowannen su zai kula da su.

Waɗannan naɗe-naɗe sun zo ne a daidai lokacin da kuɗaɗen shigar Nijeriya daga fitar da iskar gas zuwa ƙasashen waje ke ƙaruwa.

Bayanan CBN sun nuna cewa Nijeriya ta samu dala biliyan 2.53 daga fitar da iskar gas zuwa ƙasashen waje a zangon farko na shekarar 2026.

Previous Post

CBN ya nemi haɗin gwiwar bankuna da kamfanonin sadarwa domin yaƙi da ‘yan damfara da zambar kuɗi

Next Post

Sabon Ɗanmasanin Sakkwato, Farfesa Mansur, ya naɗa sarautun musamman

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Sabon Ɗanmasanin Sakkwato, Farfesa Mansur, ya naɗa sarautun musamman

Sabon Ɗanmasanin Sakkwato, Farfesa Mansur, ya naɗa sarautun musamman

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!