Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin bankuna, kamfanonin sadarwa, masu samar da fasahar zamani da hukumomin tsaro domin yaƙi da damfarar kuɗi.
CBN ya yi gargaɗin cewa masu aikata laifukan kuɗi na amfani da giɓin musayar bayanai wajen karkatar da kuɗaɗen sata ta bankuna da cibiyoyin kuɗi daban-daban.
Daraktar Fasahar Sadarwa ta CBN, Omoyemen Jide-Samuel, ce ta yi wannan kiran a ranar Laraba, yayin gabatar da jawabi a rana ta biyu ta taron ƙasa da ƙasa kan tsaron intanet karo na biyu, wanda aka gudanar a Abuja.
Lokacin da take jawabin, ta ce dangane da matsalar ƙirƙirar ƙagaggun shaidu da sabbin barazana ga tsarin kuɗi a ƙasa, dole ne cibiyoyin kuɗi su daina dogaro da binciken damfara a tsakanin su kawai, su koma tsarin musayar bayanan sirri da haɗin kai wajen ɗaukar matakan gaggawa.
Ta ce: “Dole ne a mayar da bayanan sirri da ake musayar wa zuwa matakan haɗin gwiwa. Masu aikata laifuka suna cin moriyar yadda kowace hukuma ke binciken abubuwan da ake zargi ita kaɗai.”
Jide-Samuel ta bayyana cewa damfara na iya farawa a wani banki, ta ratsa wasu bankuna da dama, sannan ta haɗa da hanyoyin sadarwa kafin a fara gudanar da binciken ƙorafin wanda aka zalunta.
Ta ƙara da cewa: “Cibiyoyin kuɗi, kamfanonin sadarwa, masu samar da fasaha, hukumomin tsaro da masu kula da harkokin kuɗi, kowannen su na da wani ɓangare na bayanan da ake buƙata. Don haka, dole ne mu haɗa waɗannan bayanai cikin gaggawa domin ɗaukar matakin da zai iya sauya sakamakon lamarin.”
Daraktar ta bayyana cewa alƙaluman Hukumar Kula da Tsarin Biyan Kuɗi tsakanin Bankuna ta Nijeriya (NIBSS) sun nuna cewa asarar kuɗaɗen da aka yi sakamakon damfarar kuɗi ta hanyar biyan kuɗi ta intanet ta ragu daga naira biliyan 52.6 a shekarar 2024 zuwa naira biliyan 25.85 a shekarar 2025, wanda ke nuna raguwar kusan kashi 51 cikin 100.
Binciken alƙaluman ya nuna cewa an samu raguwar asarar kuɗi da naira biliyan 26.75 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, duk da cewa jimillar kuɗaɗen da aka yi asarar su a cikin shekarun biyu ya kai naira biliyan 78.45.
Ta bayyana raguwar a matsayin wani gagarumin ci gaba, amma ta yi gargaɗin cewa sauran asarar da ake samu na ci gaba da shafar harkokin kasuwanci, gidaje da amincewar jama’a ga tsarin hadahadar kuɗi ta intanet.
Gargaɗi Kan Damfara ta Hanyar Amfani da Fasahar AI:
Jide-Samuel ta nuna damuwa kan yadda masu aikata damfara ke amfani da ƙirƙirar fasahar AI, musamman wajen ƙirƙirar ƙagaggun bayanan shaidar mutum ta hanyar haɗa sahihan bayanan mutane da na bogi.
Ta bayyana cewa masu laifi na iya sauya hotuna, kwaikwayon muryoyin mutane da ƙirƙirar takardun bayanan kuɗi na bogi masu kama da na gaskiya domin yaudarar cibiyoyin kuɗi su amince da hada-hadar kuɗin da aka ƙulla da zamba.
Ta yi gargaɗin cewa: “Jin muryar da aka saba da ita ba ya isa ya tabbatar da cewa wanda ake ji yana da ikon bayar da umarni.”
Saboda haka, ta buƙaci bankuna su riƙa tabbatar da sahihancin umarnin biyan kuɗi masu muhimmanci ta wasu hanyoyi masu zaman kan su, tare da ci gaba da tantance bayanan kwastomomi da yadda suke gudanar da hada-hadar kuɗi.
Ta ƙara da cewa ya kamata cibiyoyin kuɗi su samar da tsare-tsare bayyanannu kan yadda za su tuntuɓi bankunan da aka tura kuɗi zuwa gare su, adana hujjoji, taimaka wa kwastomomi da kuma kai rahoton hadahadar da ake zargi ga hukumomin da suka dace, har ma a lokutan da ba na aikin bankuna ba.







