Magoya bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ƙarƙashin kamfen ɗin “Tinubu Must Go Again 2027” (TMGA 2027), sun gudanar da wani gagarumin gangami a birnin Yola, Jihar Adamawa, yau Alhamis, jihar da ɗan siyasar adawa Atiku Abubakar ya fito daga cikin ta.
Masu shirya taron sun bayyana yawan jama’ar da suka halarta a matsayin alamar goyon bayan da shugaban ke da shi a Arewa-maso-Gabas.
Taron, wanda aka gudanar a gidan sinima na Lamiɗo, ya samu halartar magoya baya da wakilai daga jihohi shida na Arewa-maso-Gabas.
Masu shirya gangamin sun ce taron yana a daga cikin ƙoƙarin mayar da martani ga ra’ayoyin da ke cewa Shugaba Tinubu ba shi da isasshen goyon baya a Arewa gabanin zaɓen 2027.
Da yake jawabi a wajen taron, Kodinetan Ƙasa na TMGA 2027, Farfesa Sheriff Almuhajir, ya ce an shirya gangamin ne bisa zaɓin ƙashin kai domin nuna goyon baya ga shugaban ƙasa da kuma wayar da kan ‘yan Nijeriya game da manufofin gyaran tattalin arzikin gwamnatin sa.

Ya ce: “Mun zo ne domin sanar da ‘yan Nijeriya cewa Arewa ta fahimci tarihin ƙasar nan da kuma hanyar da cigaban ta ya bi. Nijeriya ta samu cigaban ta ne sakamakon gudunmawar shugabanni daga yankuna daban-daban, kuma muna ganin ya kamata ƙasar ta ci gaba da kasancewa ɗaya.”
Farfesan, wanda ya ƙware a fannin gudanar da tattalin arziki da harkokin kuɗi, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi la’akari da ƙalubalen tattalin arzikin ƙasar nan a cikin tsarin gyare-gyaren da gwamnatin take aiwatarwa.
Ya ce, a ra’ayin gangamin, ɗaukar matakai masu wahala na iya zama wajibi domin samar da sauyi mai ma’ana da kuma aza harsashin cigaba mai ɗorewa.
Almuhajir ya yi nuni da gudunmawar da Tinubu ya bayar wajen tallafa wa ‘yan siyasar Arewa, yana mai cewa shugaban ya taɓa goyon bayan ‘yan takara uku daga yankin, biyu daga cikin su kuma ‘yan asalin Jihar Adamawa ne. Ya ce hakan na nuna irin goyon bayan da Tinubu ya bai wa burin siyasar shugabanni daga Arewa.
Kodinetan ya bayyana yawan jama’ar da suka halarci gangamin a matsayin martani ga masu cewa ba za a iya samun gagarumin goyon bayan Tinubu a Arewa ba.
“Dubban matasa maza da mata sun yi tattaki sama da kilomita ɗaya domin nuna goyon bayan su ga gangamin, yayin da jama’a suka riƙa nuna goyon baya a kan hanya. Mun san shugaban yana da magoya baya a Yola, amma ba mu yi tsammanin irin wannan ɗimbin jama’a ba,” inji shi.
A nasa jawabin, Sakataren jam’iyyar APC na Jihar Adamawa, Mustapha Atiku Ribaɗu, ya ce daɗaɗɗiyar dangantakar siyasa tsakanin Tinubu da jihar, tare da ayyukan ababen more rayuwa na Gwamnatin Tarayya, suna daga cikin dalilan cigaba da neman goyon bayan al’umma.
Ya ce: “Mun ƙudiri aniyar tattara kan al’ummar mu domin goyon bayan wa’adin sa na biyu. Za mu zaɓi APC daga sama har ƙasa.”

Shi ma Mataimakin Shugaban APC na Jihar Adamawa, Dakta Raymond Chidama, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar na jihar, ya gode wa shugabannin gangamin bisa zaɓar Adamawa a matsayin wurin fara wannan shirin wayar da kai da neman goyon baya.
Mashirya gangamin sun ce taron Yola wani ɓangare ne na dabarun su na ƙasa baki ɗaya domin hulɗa da matasa, mata, ƙwararru da shugabannin al’umma gabanin zaɓen 2027, tare da yaɗa saƙon cigaba, zaman lafiya da wadata a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.







