Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Nijeriya na shirin dasa bishiyoyi biliyan 20 tun daga lokacin damina mai zuwa, a wani yunƙuri na farfaɗo da muhalli, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa ɓangaren noma na ƙasar.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin rangadin gonaki da cibiyoyin noma a yankin Oromia na ƙasar Habasha, a matsayin wani ɓangare na shirin musayar ƙwarewa tsakanin shugabannin Nijeriya da Habasha.
Ya ce Nijeriya za ta yi koyi da darussan da aka koya daga shirin Green Legacy Initiative na Habasha, wanda ya haɗa da farfaɗo da muhalli tare da samar da fa’idodin tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bayyana sauye-sauyen da Habasha ta samu a fannin noma a matsayin abin koyi ga Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika da ke neman wadatar da kan su da abinci da kuma rage dogaro da kayan abinci da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
A cewar sa, Nijeriya na da niyyar rungumar ingantattun iri, amfani da injinan noma, hanyoyin noma masu jure sauyin yanayi da kuma dabarun noma na zamani domin faɗaɗa samar da amfanin gona da ƙarfafa samar da isasshen abinci.
“Za mu ƙaddamar da gagarumin shirin dasa bishiyoyi a lokacin damina mai zuwa. Wannan na buƙatar kyakkyawan shiri, ƙwazo da jajircewa, waɗanda Habasha ta yi nasarar zaburar da al’ummar ta wajen aiwatarwa. Muna da niyyar dasa bishiyoyi biliyan 20,” inji shi.

Shettima ya bayyana samar da isasshen abinci a matsayin muhimmin ginshiƙi na ikon ƙasa na cin gashin kanta, yana mai gargaɗin cewa dogaro da kayan abinci daga ƙasashen waje fiye da kima na iya raunana ‘yancin kai na ƙasa.
“Dogaro da abinci daga ƙasashen waje na raunana ikon mu na cin gashin kanmu. Idan ƙasa ba ta da ‘yancin samar da abincin ta, to ba ta cika samun cikakken ikon cin gashin kanta ba,” in ji shi.
Ya ce Nijeriya da Habasha suna da albarkatun noma da damar tattalin arziki da za su ba su damar taka muhimmiyar rawa wajen samar da abincin da zai ciyar da Afirka, yana mai kira ga ƙasashen biyu da su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen samar da abinci mai yawa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya yaba wa Habasha bisa nasarar da ta samu wajen sauya ɓangaren noman alkama daga dogaro sosai da shigo da shi daga ƙasashen waje zuwa wadatar da kanta.
Ya lura cewa ƙasar ta fara fitar da ragowar alkamar da take samarwa zuwa ƙasashe maƙwabta, ciki har da Djibouti da Kenya.
Haka kuma, ya yaba da ci gaban da Habasha ta samu wajen ƙoƙarin wadatar da kanta da shinkafa, yana mai bayyana ci gaban da ƙasar ta samu a fannin noma a matsayin abin nasara da ya cancanci a yi koyi da shi.
“Na cika da farin ciki ganin cewa farfaɗowar tattalin arzikin Afrika na gaskiya na gab da tabbata. Habasha ta zama jagora kuma mai sahun gaba wajen ƙoƙarin mu na dawo da martabar mu da ta nahiyar mu. Muna matuƙar alfahari da ita,” in ji Shettima.
“Dole ne Afrika ta koyi ciyar da kanta. Habasha na yin hakan, kuma Nijeriya tana kan hanyar cimma wannan buri. Habasha ta samu nasarar da ta cancanci a yi koyi da ita.”
Ya bayyana noma a matsayin wani fanni da zai amfani Nijeriya da Habasha baki ɗaya, yana mai jaddada cewa ƙasashen biyu za su iya koyon darussa daga gogewar juna domin inganta rayuwar al’ummomin su.
Shettima ya kuma yi kira ga sauran ƙasashen Afrika da su rungumi wasu daga cikin dabarun noma na yankin Oromia na Habasha, wanda ke amfani da faɗin filayen noma da kuma bambancin yanayin wurare wajen ƙara yawan amfanin gona da samar da kuɗaɗen shiga ta hanyar fitar da kayayyakin noma zuwa ƙasashen waje.
Ya ce ƙara kusantar juna da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu na iya inganta samar da isasshen abinci a faɗin nahiyar, musamman idan aka yi la’akari da cewa jimillar al’ummar su ta haura mutum miliyan 400.
“Tare da al’ummar mutum miliyan 100, da kuma haɗin gwiwar al’ummar ta da ta Nijeriya wanda ya haura mutum miliyan 400, nasarar Habasha za ta yi tasiri a faɗin Gabashi da Kudancin Afrika,” inji shi.
Tun da farko, Shugaban Gwamnatin Yankin Oromia, Shimelis Abdisa, ya yi bayani kan nasarorin da Habasha ta samu a fannin noma da kuma gudunmawar da ɓangaren ke bayarwa ga tattalin arzikin ƙasar.
Abdisa ya ce ana noma nau’ikan amfanin gona sama da 200 a faɗin Habasha, yayin da ƙasar ta faɗaɗa fitar da kayayyakin noma zuwa ƙasashen waje, ciki har da ayaba, avokado da kofi.
Ya ƙara da cewa noman alkama na samar da kuɗaɗen shiga da suka haura dala biliyan 3.1 a duk shekara, yana mai cewa alkamar Habasha tana iya gogayya da ta sauran ƙasashe a kasuwannin duniya.
Shugaban yankin na Oromia ya kuma bayyana cewa yankin na haɗin gwiwa da rukunin kamfanonin Dangote wajen samar da takin zamani ga manoman yankin.
Ya ce masana’antar kiwon kaji ta yankin ta samu gagarumin bunƙasa fiye da ƙarfin da take da shi na farko, wato kaji miliyan biyu, yayin da ake shirin ƙara faɗaɗa ta.
A yayin ziyarar, Shettima ya zagaya gonakin alkama, ayaba da gwanda, inda ya duba tsarin noman Habasha da kuma ƙoƙarin da take yi na ƙara yawan abincin da take samarwa.







