Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhinin sa bisa rasuwar Sakatare-Janar na Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Nijeriya (SCSN), Malam Nafi’u Baba-Ahmed, wanda ya rasu da sanyin safiyar yau Talata bayan tsawon shekaru yana hidimta wa Musulunci da ƙasa.
Shugaban ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tasiri, wanda ya jagoranci harkokin Majalisar Ƙoli ta Shari’a cikin hikima, hangen nesa da kishin haɗin kan al’umma, adalci da zaman lafiya.
Tinubu ya tuna da doguwar alaƙar da ke tsakanin sa da marigayin, musamman tun daga shirye-shiryen zaɓen shekarar 2011, da kuma shekarun baya, inda Malam Baba-Ahmed ya kasance cikin waɗanda suka ba shi shawarwari tare da mara masa baya a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
A cewar sa, marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa Majalisar ta ci gaba da bayar da gudunmawar ta kan muhimman batutuwan ƙasa, tare da ƙarfafa fahimtar juna da kuma yaɗa kyawawan ɗabi’u, adalci da gyaran zamantakewar al’umma.
Shugaban Ƙasar ya miƙa ta’aziyyar sa ga Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya, shugabanni da membobin ta, iyalan Baba-Ahmed, gwamnatin da al’ummar Jihar Kaduna, da kuma ɗaukacin al’ummar Musulmi a Najeriya bisa wannan babban rashi.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kurakuran sa, Ya jikan sa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalan sa da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.







