Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi magana kan shirun da wasu tsofaffin abokan aikin sa da abokan sa da mutanen da suka taɓa hulɗa da shi suka yi a yayin da yake fuskantar halin da yake ciki a yanzu, yana mai cewa lokutan ƙalubale sun ba shi damar fahimtar dangantakar sa da mutane cikin ƙarin haske.
A cikin wata sanarwa mai taken “Dangantaka ta da abin da ya biyo baya”, El-Rufai ya ce ya kasance yana tarayya da mutane da kuma manufofin da ya yi imani da su ba tare da tsammanin yabo, godiya ko goyon baya daga gare su ba. Ya ce imanin sa, ƙa’idojin sa na ƙashin kan sa da kuma lamirin sa ne suka jagoranci irin waɗannan matakai da ya ɗauka.
A cewar sa, mutanen da ya taɓa tallafa wa suna da ’yancin yanke shawarar ko za su yi magana, su yi shiru ko kuma su nisanta kan su daga dangantakar da ta kasance tsakanin su a baya.
Ya ƙara da cewa abubuwan da ya fuskanta a cikin watannin baya-bayan nan na iya sa shi sake yin nazari a hankali kan wasu daga cikin dangantakar sa da mutane, yana mai jaddada cewa hakan ba yana nufin yana yin nadama da su ba.
Tsohon gwamnan ya ce bai yi nadamar tallafa wa mutane a lokacin da ya yi imanin cewa abin da ya dace kenan ba, kuma ba ya jin haushi ko ƙiyayya ga waɗanda suka zaɓi ba su yi masa irin wannan ba.
Ya kuma ce ba ya neman ɗaukar fansa ko yin sakayya, domin ya bar hukunci da hisabi na ƙarshe ga Allah Maɗaukakin Sarki.






