Fassara: Mairo Muhammad Mudi
An naɗa Uwargidan Gwamnan Jihar Neja, Hajiya Fatima Mohammed Bago, matsayin Babbar Uwar Ƙungiyar Mata ’Yan Kasuwa Masu Tasiri ta Shirin Renewed Hope Agenda (Business Women of Influence for Renewed Hope Agenda, BWI/RHA), reshen Jihar Neja.
Daraktar Yaɗa Labarai ta reshen ƙungiyar, Rose Nnatasa Jiya, ta faɗa a cikin wata sanarwa cewa an gudanar da bikin naɗin tare da karramawar ne a Minna, inda Ko’odinetan ƙungiyar ta Jihar Neja, Misis Mary Noel Berje, ta gabatar da naɗin Hajiya Fatima Bago tare da bayyana cewa an ba ta wannan matsayi ne bisa la’akari da irin gudunmawa da jajircewar da take nunawa wajen ƙarfafa gwiwar mata da tallafa musu a faɗin jihar.
Misis Berje ta bayyana cewa BWI/RHA ƙungiya ce da Dakta Ngozi Oyewole, Darakta Janar kuma wadda ta assasa ƙungiyar, ta kafa da nufin haɗa kan mata, ƙarfafa musu gwiwa da kuma tallata mata ’yan kasuwa da ƙwararru.
Ta ce baya ga wannan, ƙungiyar tana ƙoƙarin ciyar da manufofi da ƙudirorin Shirin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu gaba.
Ta ƙara da cewa a halin yanzu reshen ƙungiyar na Jihar Neja yana gudanar da wani bincike na musamman mai suna “Community Skills Census” a ƙananan hukumomi 25 na jihar domin gano tare da tattara bayanai kan sana’o’i, ƙwarewa da damar kasuwanci da mata ke da su.
A cewar ta, bayanan da za a tattara za su taimaka wajen gano ɓangarorin da mata ke buƙatar tallafi, waɗanda suka haɗa da koyon sana’o’i, samun jari, shawarwari da jagoranci, samun kasuwanni, da kuma ƙara ilimi da ƙwarewa.
Ta jaddada cewa babban burin kungiyar shi ne taimaka wa mata su dogara da kan su ta fuskar tattalin arziki, tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arziki da cigaban Jihar Neja.
Da take mayar da martani bayan naɗin, sabuwar Babbar Uwar kungiyar ta Jihar Neja, Hajiya Fatima Mohammed Bago, ta gode wa ƙungiyar bisa ganin ta cancanci wannan matsayi.
Ta kuma bayyana shirin ta na haɗa hannu da BWI/RHA domin cimma manufofin ƙungiyar, tare da yin kira da a mayar da hankali kan shirye-shiryen da za su samar da sauyi na zahiri kuma mai ɗorewa a rayuwar mata, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara.







