• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, ra Rasu yana da shekaru 90

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
September 12, 2026
in Labarai
A A
0
Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, ra Rasu yana da shekaru 90
Marigayi Alhaji Bamanga Mohammed Tukur

Marigayi Alhaji Bamanga Mohammed Tukur

Tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na Ƙasa, Alhaji Bamanga Mohammed Tukur, ya rasu yana da shekaru 90.

Tukur ya rasu ne yau Asabar, 12 ga Satumba, 2026, a cewar wata sanarwa da iyalan sa suka fitar, wadda ɗan sa, Awwal D. Tukur, ya sanya wa hannu.

Iyalan sa sun bayyana tsohon shugaban na PDP a matsayin “uba kuma jagoran iyali abin ƙauna”, suna cewa ya sadaukar da rayuwar sa wajen yi wa iyalin sa, al’ummar sa, Jihar Adamawa da Nijeriya hidima.

“Cikin tsananin baƙin ciki da cikakkiyar miƙa wuya ga ikon Allah Maɗaukaki, iyali suna sanar da rasuwar uban mu kuma jagoran iyali abin ƙauna, Alhaji Bamanga Mohammed Tukur, wanda ya koma ga Mahaliccin sa a yau, 12 ga Satumba, 2026,” inji sanarwar.

Iyalin sun nuna godiyar su ga dukkan waɗanda suka yi musu addu’o’i, ta’aziyya da kuma goyon baya bayan rasuwar tasa.

Sun ce za a ba da sanarwar lokacin Sallar Jana’iza da sauran shirye-shiryen binne mamacin nan gaba.

“Mun roƙi Allah Maɗaukaki ya gafarta masa kurakuran sa, ya karɓi kyawawan ayyukan sa, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdausi,” inji iyalin.

An haifi Bamanga Tukur ne a ranar 15 ga Satumba, 1935, kuma da ya rayu, zai cika shekaru 91 bayan kwana uku kacal da rasuwar sa.

Ya taɓa zama Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, sannan ya riƙe muƙamin Ministan Masana’antu a lokacin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha.

Tukur ya taɓa zama Babban Manajan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) kuma Babban Darakta, baya ga riƙe wasu muƙamai a harkokin kasuwanci da kuma fafutukar bunƙasa tattalin arzikin Afrika.

A watan Maris na 2012 ne aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.

Zaman sa a matsayin shugaban jam’iyyar ya zo ne a wani lokaci da PDP take fama da rikice-rikicen cikin gida, waɗanda daga bisani suka kai ga ɓullar ƙungiyar “New PDP” a shekarar 2013.

Tukur ya yi murabus daga shugabancin PDP a Janairu 2014, a daidai lokacin da rikicin cikin jam’iyyar ke ƙara tsananta.

Daga bisani, gwamnatin Jonathan ta naɗa shi Ambasada na Musamman (Ambassador-at-Large).

Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

Next Post

Nijeriya za ta yi kewa – Tinubu ya yi jimamin rasuwar dattijo Bamanga Tukur

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Nijeriya za ta yi kewa – Tinubu ya yi jimamin rasuwar dattijo Bamanga Tukur

Nijeriya za ta yi kewa - Tinubu ya yi jimamin rasuwar dattijo Bamanga Tukur

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!