• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
September 10, 2026
in Siyasa
A A
0
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Shugabannin APC na ƙananan hukumomi 25 na Jihar a lokacin ziyarar su ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, domin jaddada goyon baya ga tsare-tsare da manufofin gwambatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a Abuja yau Alhamis  (HOTO: Adnan) Suleiman/FMINO

Shugabannin APC na ƙananan hukumomi 25 na Jihar a lokacin ziyarar su ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, domin jaddada goyon baya ga tsare-tsare da manufofin gwambatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a Abuja yau Alhamis  (HOTO: Adnan) Suleiman/FMINO

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Neja da su mara wa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya tare da taimakawa wajen ƙarfafa nasarorin da aka samu a tattalin arziki, tsaro, ababen more rayuwa, ilimi da bunƙasa ƙwarewar ’yan Nijeriya.

 

Idris ya yi wannan kiran ne ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya karɓi shugabannin APC na ƙananan hukumomi 25 na Jihar Neja, waɗanda suka kai masa ziyarar nuna goyon baya.

 

Ya ce: “Dole ne dukkan mu mu haɗa hannu da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya ƙarfafa nasarorin da muka riga muka samu, tare da ɗora Nijeriya kan ingantaccen turbar tattalin arziki”.

 

Ministan ya ce Tinubu ya gaji ƙasar cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki da tsaro lokacin da ya hau mulki a watan Mayu 2023, yana mai cewa tattalin arzikin ƙasar nan yana fuskantar matsin lamba sosai, yayin da rashin tsaro ya yi matuƙar shafar rayuwa da sana’o’in ’yan Nijeriya.

 

“Yana da sauƙi a manta da inda muka fito, amma a yau wannan yanayi ya sauya sosai. Yanzu muna da ƙarin damar gudanar da ayyukan ci gaba da ’yan Nijeriya ke gani a sassa daban-daban na ƙasar,” inji Idris.

 

Ya ce cire tallafin man fetur ya samar da ƙarin kuɗaɗe da gwamnati ke amfani da su wajen saka jari a noma, hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi da ci gaban matasa, yayin da sauye-sauyen gwamnati ke taimakawa wajen dawo da amincewar masu zuba jari.

 

Idris ya kuma ambaci manyan ayyukan ababen more rayuwa, ciki har da Babbar Hanyar Tekun Lagos zuwa Kalaba da Babbar Hanyar Sakkwato zuwa Badagiri, yana mai cewa ana ci gaba da gina hanyoyi a faɗin ƙasar nan.

 

Dangane da tsaro, ya amince da cewa har yanzu akwai ƙalubale, amma ya ce ƙasar nan tana samun cigaba a hankali wajen dawo da zaman lafiya.

 

“Shin mun kai inda muke so? A’a. Shin har yanzu muna fuskantar ƙalubale? E. Amma shin muna ganin cigaba a hankali wajen dawo da zaman lafiya a ƙasar nan? E,” inji shi.

 

Ministan ya kuma ambaci Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), yana mai cewa sama da matasa ’yan Nijeriya miliyan ɗaya sun samu damar yin karatun gaba da sakandare ta hanyar shirin.

 

Ya buƙaci shugabannin na APC da su ci gaba da haɗa kai tare da warware saɓanin da ke tsakanin su ta hanyar tattaunawa, yana mai jaddada muhimmancin mayar da hankali wajen ƙarfafa wa gwamnati gwiwa da kuma ci gaba da ajandar cigaban ta.

 

“Ya kamata ’yan Nijeriya su yi watsi da duk wani yunƙuri na mayar da mu zuwa wancan zamanin na rashin tabbas,” inji Idris.

 

Shugaban tawagar kuma Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin APC na Jihar Neja, Hon. Hashimu Izom, ya taya Idris murnar naɗa shi minista tare da yaba masa kan yadda yake wakiltar Jihar Neja a matakin tarayya.

 

Izom ya yaba wa ministan kan ƙoƙarin sa na ƙarfafa haɗin kan jihar da kuma tallafa wa ayyuka da shirye-shiryen da ke amfanar al’ummar Neja.

 

Ya ce: “Muna alfahari da kai, ba don kai ne Mohammed Idris Malagi ba, amma saboda kai ɗan asalin Neja ne na haƙiƙa, wanda a duk inda yake yana tsayawa tsayin daka wajen kare Shugaban Ƙasa da wakiltar Jihar Neja har a matakin ƙasa.”

Previous Post

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

Next Post

Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, ra Rasu yana da shekaru 90

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ce babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, jama’a su kwantar da hankalin su
Siyasa

Mayar da tallafin man fetur zai mayar da Nijeriya baya — Idris

August 24, 2026
Next Post
Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, ra Rasu yana da shekaru 90

Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, ra Rasu yana da shekaru 90

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!