• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
September 9, 2026
in Siyasa
A A
0
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Daga dama: Shugaban ƙungiyar Charismatic Bishops Conference of Nigeria, Archbishop Leonard Bature Kawas; wakilin Shugaban Ƙasa kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; wakilin Uwargidan Shugaban Ƙasa kuma Shugaban CAN na Jihar Legas, Bishop (Dr.) Stephen Adegbite, yayin ƙaddamar da llittafin 'Nigerian National Prayer Handbook', wanda Archbishop Prof. Leonard Bature Kawas ya rubuta, a babban taron ƙarshe na Synod na 2026 na CBCN, a ranar 9 ga Satumba, 2026, a Abuja. (Hoto: Khalid Ahmed/FMINO)

Ƙungiyar “Charismatic Bishops Conference of Nigeria” (CBCN) ta bayyana goyon bayan ta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.

Shugaban CBCN, Archbishop Prof. Leonard Bature Kawas, shi ne ya bayyana matsayar ƙungiyar a ranar Laraba a Abuja, a lokacin da ake gudanar da babban taron Synod na 2026 na CBCN da ICCABA a Majami’ar Kiristoci ta Ƙasa.

Kawas ya ce ƙungiyar ta yi nazari kan ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da bayyana shirin ta na ci gaba da mara wa shugaban ƙasar baya ta hanyar addu’a, bayar da shawarwari da kuma wayar da kai.

Ya ce: “Mun goyi bayan sa a yanzu. Mun goyi bayan sa yau, za mu goyi bayan sa gobe, kuma za mu ci gaba da goya masa baya muddin yana son kasancewa shugaban ƙasar mu.”

Ya ƙara da cewa: “Wannan gida ya amince da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.”

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci shugabannin addini da su yi amfani da tasirin su wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da kyakkyawar mu’amala tsakanin al’umma gabanin zaɓen 2027.

Ya ce: “Ci gaba da haɗa kan wannan ƙasa na buƙatar fiye da matakan gwamnati. Yana buƙatar jagoranci nagari daga dukkan ɓangarorin al’umma, ciki har da jagorancin addini.”

Idris ya yi gargaɗi kan yunƙurin nuna matsalolin tsaron Nijeriya a matsayin yaƙin addini, yana mai cewa ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun kai wa ’yan Nijeriya hare-hare ba tare da la’akari da addinin su ko asalin su ba.

“Kada a bari wani zaɓe ya sa Kirista ya juya wa Musulmi baya, ko Musulmi ya juya wa Kirista baya, ko Arewa ta juya wa Kudu baya, ko wata ƙabila ta juya wa wata baya. Nijeriya tamu ce baki ɗaya,” inji shi.

Da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Tinubu, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya yaba wa ma’abota cocin kan gudunmawar su ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da kira da a samu ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin addini.

Ya ce: “Gwamnati tana buƙatar gudunmawar Kiristoci wajen kyautata ɗabi’a da tarbiyyar al’umma, yayin da Kiristoci suke buƙatar yanayin da zai ba su damar gudanar da ayyukan su da kyau. Fiye da komai, Nijeriya tana buƙatar mu yi aiki tare domin amfanin kowa.”

Previous Post

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!